Halayen Imam Bakir (a.s)



Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu.

Abu Ja’afar (a.s): To Babu komai kenan.

Sa’id: To halaka ke nan.

Abu Ja’afar (a.s): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna.

Imam Muhammad Bakir (A.S): Shi ne Muhammad Bakir dan Ali (A.S) kuma babarsa ita ce Fadima 'yar Imam Hasan (A.S) an haife shi a Madina ranar juma'a watan rajab mai alfarma, shekara ta hamsin da biyar, kuma shi ne farkon alawi da aka haifa daga alawiyyawa biyu kuma hashimi tsakanin hashimiyyawa biyu kuma fadimi tsakanin fadimiyyawa biyu, domin shi ne farkon wanda haihuwar imamami biyu ta hadu gareshi. kuma ya yi shahada ta hanyar guba a ranar litinin bakwai ga zulhajji shekara ta dari da goma sha hudu yana da shekaru hamsin da bakwai, kuma dansa Imam Ja'afar Sadik shi ne ya shirya shi ya kuma binne shi a janibin babansa Imam Sajjad (A.S) da kuma ammin babansa kuma kakansa Imam Hasan Mujtaba (A.S) a Bakiyya a Madina.

Ya kasance ma'abocin fifiko mai girma da daukaka da addini da ilimi mai yawa da hakuri mai yalwa da kyawawan halaye da ibada da kaskan da kai da baiwa da rangwame kuma ya kai karshen kyawawan dabi'u wani kirista ya ce masa: kai bakar ne. (wato; saniya)

Sai ya ce: Ni dai Bakir ne.

Sai ya ce: kai dan mai dafa abinci ne.

Sai ya ce: wannan sana'arta kenan.

Sai ya ce: kai dan bakar mace ne ballagaza.

Sai ya ce: idan ka yi gaskiya Allah ya gafarta mata, idan ka yi karya kuma Allah ya gafarta maka.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next