Halayen Imam Bakir (a.s)



Hisham ya yi hakan domin ya kubutar da Sham daga karkata zuwa ga alayen Manzon Allah (s.a.w) da kuma ci gaba da batar da su kamar yadda kakanninsa suka yi. Don haka ne sai ya kuduri muguwar aniyarsa ta korar Imam Bakir (a.s) daga wannan gari na Sham.

Sai dai kuma ya bayar da sanarwa cewa kada wanda ya sayar wa Imam da komai hatta da abinci, wannan kuwa ya yi haka ne domin ya gama da Imam Muhammad Bakir (a.s) ta yadda yunwa da wahala zasu iya kashe shi, sai ya kasance ke nan ya cimma burinsa na gamawa da shi.

A kan hanya ne Imam Bakir (a.s) ya wuce wani gari da suka ki sayar masa da abin ci da abin sha don haka ne sai ya hau kan duwatsu ya yi kira ga Allah ya kuma shelanta wa mutanen wannan kauyen cewa; Ni ne ragowar na Allah. Don haka ne wani dattijo ya gaya musu cewa idan ba su amsa wa Imam Muhammad Bakir ba, to lallai za a kisfe garin da halakarwa, domin wannan maganar tasa irin maganar Annabi Shu’aibu (a.s) ce.

Imam Bakir (a.s) ya shahara da munazarori da mutane daban-daban da suka hada musulmi da kiristoci, akwai tattaunawarsa da kuma amsa tambayoyin mutane kamar Nafi’u, da Dawus da makamantansu. An ambace shi mai tsage ilimi tsagewa saboda abin da ya yi na fede ilimi fedewa, wanda al’amari ne da shi ne farkon wanda ya samu damar yin hakan.

Lokacin Imam Muhammad Bakir zamani ne da yake cike da rikicin siyasa wanda ya shagaltar da masu mulki da rikicin da yake tsakaninsu ko kuma tsakaninsu da wasunsu a lokuta daban-daban, don haka ne wannan lamari ya ba wa Imam Bakir (a.s) damar yada ilimi kafin ya kasance ya ci gaba da yaduwa da habaka a hannun dansa Imam Ja'afar Sadik (a.s).

Rikin da ya damu masu mulki ya sanya su nesa da malamai da ilimi da yi musu hidima, sai ilimi ya yi kasa matukar gaske, sai wannan ya kasance wata dama a wani bangare ga shi Imam Bakir (a.s) domin ya habaka ilimin makarantar Manzon Allah (s.a.w) da ya gada daga kakanninsa (a.s). Sannan ta wani bangaren wannan raunin ya sanya hujumin wadanda suke ganin sun samu damar da za su iya murkushe musulunci cikin sauki, sai dai ludufin Allah na samar da alayen manzonsa a matsayin masu kariya ga wannan addinin ya sanya samuwar Imam Bakir ta yi maganin wadancan ma’abota addinai da mazhabobin da suka so yi wa musulunci kwaf daya.

Don haka ne ma kafin Imam Muhammad Bakir ya yi wafati ya yi wa dansa magandinsa Imam Ja'afar Sadik (a.s) wasiyya da karfafar tafarkin da ya fara wanda shi ne damar da aka samu tun bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w). kamar yadda ya yi wasiyya ga mafi yawan sahabbansa kamar yadda ya zo a wasu littattafan.

Kasancewar musulumi sun bar aiki da wasiyyar manzon rahama ta riko da littafin Allah da Ahulu Baiti (a.s) bayan wafatinsa (s.a.w), wannan lamarin ya haifar da gibi mai yawa na rashin sanin madafa wurin sanin hakikanin hukuncin shari'a. Don haka sai aka samu mutane iri-iri da suka dauki nauyin ganin sun fitar da hukuncin shari'a.

Amma sai ya zamanto sun rasa sanin mafi yawan hukuncin sakamakon karancin hadisai da suke hannun al'umma. Idan ba mu manta ba, a farkon halifancin halifa na farko, halifa na biyu ya sanya an tara duk wasu hadisai na manzon Allah (s.a.w) ya kona su, sannan kuma ya hana bayar da hadisai ga kowane mutum, hasali ma ya yi wa wasu sahabbai bulala sakamakon suna bayar da hadisai. (Dabakatul Kubura: Ibn Sa'ad; 1 / 140, Hujjiyatus Sunna: 395, Kanzul Ummal: 1/291).

Amma Imam Ali (a.s) da dalibansa, da wasu sahabbai daga masu ilimi sun ki hanuwa, suka ci gaban da bayar da hadisai, kodai a boye, ko bayyane, don haka ne ruwaito hadisi bai yanke ba a tsakanin daliban imam  Ali (a.s) da koyarwarsa. Wannan lamarin bai boyu ba kuma a fili yake zamu iya ganin sa a cikin maganganun Abuzar. (Buhari: 1/27, Fathul Bari: 18/170, Sunan Darimi: 1/112, Wudhu'un Nabi: Shahristani; j 2, shafi 21-22).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next