Halayen Imam Bakir (a.s)



Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da bayanin halayen Imam Muhammad al-Bakir (a.s) da rayuwarsa.

Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da yake kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Imam Bakir (a.s) ya gaji makarantar babansa Imam Ali Zainul-abidin (a.s) kuma ta habbaka a hannunsa yayin da ta kasance makoma da dukkan musulmi suke komawa zuwa gareta, har ta kai kolinta a hannun Imam Sadik (a.s) bayansa.

Wannan makaranta ita ce ta haifar da fikihu mai zurfi na shi’a da malamai dubunnai da suka yadu suka yada ilimi a duniya baki daya a dukkan fagen ilimi, sannan kuma ta rike koyarwa da ilimin addini daga bacewa gaba daya, sai dai da yawa daga wadanda suka fita daga wannan makaranta wasu sun gina nasu makarantun abin da ya haifar da makarantu masu yawa da mahangai daban-daban.

Siyasar wannan zamani ta Banu Umayya ba a boye yake ba cewa tana son gamawa da Imam Bakir (a.s) kuma wannan yunkurin nasu ne ya kai su ga neman ganin bayansa a lokuta mabambanta da kiran sa zuwa Sham domin a samu wani laifi da aka lika masa wanda zai ba su damar gamawa da shi.

Fadar Hisham ta so yin isgili da Imam Bakir (a.s) kuma ta yi mada dariya yayin da Hisham ya yi masa isgili da cewa yaushe ne zaku daina kiran cewa ku ne jagororin al’umma. Amma sai Imam Muhammad Bakir (a.s) ya nuna musu cewa idan suna da mulkin wannan duniya a yau to su sani cewa alayen Annabi (s.a.w) suna da shi a karshenta ne, kuma babu wanda zai sake yin mulki bayan sun yi a karshen duniya.

Haka nan Imam Bakir (a.s) ya fita yana mai kunyata su. Sai dai yayin da ya ga mutane fada sun tsananta suna gaya wa mutanen Sham cewa wannan fa jikan Ali (a.s) ne domin mutanen Sham su dauke shi a matsayin makiyinsu sai ya ga ya dace ya lurasshe da su ya kuma sanar da su waye Ali (a.s) kuma su waye alayen Manzon Allah (s.a.w) don haka ne sai ya yi musu kalamai masu ratsa jikinsu da suka sanya su shiga cikin hankulansu da rena kawukansu saboda jahiltar su da addini da ahalinsa.

Da gaske hudubobin da Imam Bakir (a.s) ya yi sun ratsa mutanen Sham don haka ne sai falalarsa ta yadu a cikinsa, kowane kwararo da sako sai maganar iliminsa da takawarsa da nutsuwarsa da kwarjininsa, da baiwarsa ake yi, don haka wannan sai ya sake tayar da mugun nufin nan na fushin Hisham sai ya tsare shi a gidan kaso.

Amma kuma wannan sai ya zama aibi ga Hisham da kuma kisan mummuke da ya yi wa kansa, domin Imam Bakir (a.s) ya mayar da mutanen da suke kurkuku muminai masana ga Allah masu jin tsoronsa kuma masana da hakikanin sakon Manzon Allah (s.a.w) cikin dan kankanin lokaci, ganin haka ne sai Hisham ya gaggauta sakinsa da mayar da shi Madina babu shiri.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next