Halayen Imam Bakir (a.s)



5. Bore da yunkurin Alawiyyawa daya bayan daya da nufin kifar da gwamnatin Umayyawa.

6. Bin son zuciyar da mafi yawancin shugabannin Umayyawa suka yi. Da sabawarsu ga shari'ar Musulunci a cikin dabi'unsu.

7. Rashin ko in kula ta Umayyawa a game da matakin musulmi na rashin amincewa da su. Da kuma dagewar Umayyawa a kan ayyukansu munana.

Daya daga cikin abin da Imam Muhammad Bakir (a.s) ya sanya gaba shi ne kokarin bayanin mene ne hakikanin shi’anci hatta ga wadanda suke ganin kansu a matsayin shi’arsu mabiyansu, kamar yadda dai ya dage wurin ganin ya sanar da al’umma mene ne musulunci, fadinsa mai daraja ya zo kamar haka:

Ya Khaisama! ka isar daga garemu cewa ba zamu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsaâ€‌[1].

Imamai masu daraja (a.s) suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya, kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare kuâ€‌[2].

A yanzu zamu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:

1- Muhawarar Abu Ja’afar Imam Muhammad Bakir (a.s) shi da Jabir Ju’ufi[3]: “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shiâ€‌.

“Su ba a gane su sai da kaskan da kai, da tsoron Allah, da rikon amana, da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai, da mabarata, da masu bashi, da marayu, da gaskiyar magana, da karatun Kur’ani, da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni.

2- Tattaunawar Abu Ja’afar (a.s) da Sa’id Bn Hasan[4]:

Abu Ja’afar (a.s) “Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next