Aure Mai Iyaka



Ibn Abbas yana cewa: Mutu'a ba komai ba ce, sai rahamar Allah ga bayinsa da ya tausaya musu da ita, ba domin Umar ya hana ba, da ba mai yin zina sai ya tsiyata (ya tabe).

Idan mun dogara da wasu littattafai da bugunsu ya zo da kalmar haka: إلاّ شفى maimakon   Ø¥Ù„اّ شقيto ma'anar maganar imam Ali (a.s) zata kasance ne kamar haka: Ba domin Umar ya hana mutu'a ba, ba wanda zai yi zina sai 'yan kadan.

Suyudi a littafinsa na Tarikhul khulafa, ya kawo cewa: Farkon wanda ya haramta auren mutu'a shi ne Umar dan Khaddabi[23].

Wannan al'amari yana nuna mana halaccinsa a asalin shari'a, duk da wasu daga malamai sun bi haramcin Umar har zuwa ranar mu wannan. Amma manyan sahabbai irinsu imam Ali suna da matakin da suka dauka sabanin haka karara.

Sannan mun ga kalmar nan mash’huriya ta Imam Ali (a.s) da yake cewa: “Ba don Umar ya hana auren mutu’a ba, da babu wanda zai yi zina sai shakiyyi (tababbe).

Ibn Hazam yana cewa: Wasu jama'a sun tabbatar da halaccinta bayan Manzo kamar: Asma'u 'yar Abubakar, da Jabri dan Abdullah, Ibn Mas’ud, Ibn Abbas, Mu’awiya dan Abu Sufyan, Abu Sa’idul Khuduri, Ibn Hurais, da Salma da Ma’abad ‘Ya’yan Umayya.

Daga Tabi’ai kuwa suna da yawa da suka hada da: Dawus, da Ada’, Sa’idu bn Jubair, Sauran malaman Makka[24].

Amma Kurdabi yana ganin cewa wasu daga sahabbai daga cikinsu akwai Umran dan Hasin, da kuma sahabban Ibn Abbas daga mutanen Makka da Yaman duk sun tafi kan halaccin auren mutu’a bisa mazhabar Ibn Abbas[25].

Haramta auren mutu'a da Umar ya yi yana daga cikin abin da imamiyya suka sanya shi daga cikin rashin cancantarsa ga halifanci, domin aikin halifa kamar yadda mai littafin Sharhul Mawakif yake fada shi ne; ya kare addini daga ragi da dadi, da kare shubuhohi da ake yi masa, ake jifan sa da su. Ba ya rushe dokokin da manzon Allah (s.a.w) ya zo da su ba, wadanda misalansu suna da yawa, kamar yadda ya zo da sababbin dokokin da suka saba wa musulunci!.

Idan muka duba dukkanin hujjojin da suke kawowa kan haramcin auren mutu'a zamu ga ba sa wuce uku:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next