Aure Mai Iyaka



·       A auren mutu'a; da dayan ma'aurata miji ko mata zai mutu, to da babu gado tsakaninsu, sai dai idan sun shardanta hakan yayin aurensu.

Auren Wata Al’umma

Idan auren wata al’umma da ba musulma ba ya kasance sabanin na musulunci, to shari’ar musulunci ta zartar da aurensu, don haka wannan matar tana da hurumin cewa tana da aure, kuma dole ne kiyaye dukkan hurumin da mace me aure take da shi game da wannan matar.

Amma a mas’alar yaki wani abu ne mai bambanci da wannan mas’alar, domin yaki yana nuni da cewa al’ummar da ta kawo hari tana son kashe jama’ar musulmi ne gaba daya, don haka ne shari’a ta halatta daukar irin wadannan mutane masu hadari a matsayin ribar yaki, matansu kuwa a matsayin bayi da ya halatta a kusance su bayan ribace su a yaki.

Sannan kana iya samun sabani tsakanin su kan su musulmi, ta yadda wani yana da fatawa a mazhabinsa da ta saba da ta wani. A nan ma dukkan mazhabobi sun tafi a kan cewa; Auren da yake bisa ijtihadin malaman mazhaba, haka ma saki da yake kan wata fatawa ta wata mazhaba dukkaninsu sun inganta.

Misalin da zan so bayarwa a nan shi ne; Idan wani mutum da yake bin mazhabar Maliki, ya saki mace ba tare da shedu biyu adalai ba, a waccan mazhabar ta Malikiyya sakin ya yi, amma a mazhabar Ahlul Bait (a.s) wannan ba saki ba ne, domin ya rasa daya daga cikin sharuddan da suka zo a cikin Kur’ani mai girma. Amma tun da a waccan mazhabar saki ne, don haka ya halatta ga wanda yake bin mazhabin Ahlul Bait (a.s) ya aure ta bayan ta gama idda; Akwai misalai masu yawa irin wannan a tsakanin mazhabobin musulunci.

Sabani Kan Auren Mutu'a

An yi sabani da yawa kan lamurran hukunce-hukuncen musulunci, wani lokaci sabanin ya kan kai ga wasu su haramta wani abu, wasu kuma su halatta shi kan lamari daya, auren mutu'a yana daga cikin abubuwan da suka samu kansu a cikin wannan yanayi. Muna iya ganin yadda Imam Musa Kazim (a.s) ya yi wa Abu Yusuful Kadhi nasiha kan yadda suka cire shedu biyu a kan saki, suka mayar da su a daurin aure, wato shedu biyu a aure Allah bai wajabta su ba, amma ya wajabta su a saki, sai suka juya lamarin.

Kamar yadda zamu iya ganin yadda Imam Bakir (a.s) ya kausasa magana kan wanda ya haramta auren mutu'a yana mai dogaro da Umar dan Khaddabi wanda shi ne ya haramta. Kana iya karanta wannan ruwayar:

Al’abi ya ce: A cikin littafin Nasruddurar: An rawaito daga Abdullahi dan Mu’ammar Allaisi ya ce da Abi Ja’afar (a.s): Labari ya zo mini cewa kai kana bayar da fatawa da yin auren mutu’a? ya ce: Allah ya halatta ta a littafinsa kuma Manzo (s.a.w) ya sunnanta, sannan sahabbansa sun yi aiki da ita, sai Abdullah ya ce: Ai Umar ya hana yin ta. Sai imam Bakir ya ce: Kai kana kan maganar sahibinka, ni kuma ina kan maganar Manzon Allah (s.a.w). Sai Abdullah ya ce: Shin zai faranta maka rai (‘ya’yan) matanka su aikata haka? Sai Abu Ja’afar (imam Bakir) (a.s) ya ce: Kai wawa? Wannan da ya halatta a littafinsa kuma ya halatta ga bayinsa ya fi ka kishi da kai da wanda ya hana, yana mai dora wa kansa nauyi, a yanzu zai faranta maka rai cewa ‘yarka tana karkashin auren wani masaki daga masakan garin Yasrib (Madina)? Sai ya ce: A’a. Sai imam (a.s) ya ce: Me yasa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa, amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai ya ce: Ai hakika Allah ya yarda da aikinsa ya so shi, ya aura masa Hurul-i’n, a yanzu kana kin wanda Allah yake son sa? kana kin wanda yake tsara na Hurul-i’n din aljanna saboda shisshigi da girman kai? Sai Abdullah ya yi dariya ya ce: Wallahi ba na ganin kirazanku (zukatanku) sai mabubbugar ilimi, sai ‘ya’yan itacensa suka zama a hannunku, ganye kuwa ya rage a hannun mutane[7].

Sahabbai Sun Yi

A fili yake cewa; musulmin farko na zamanin manzon Allah (s.a.w) da lokacin Halifa Abubakar ba su san haramcin auren mutu'a ba. Muna iya gani kusan dan farko da aka samu sakamakon auren mutu'a shi ne Abdullahi dan Zubair dan Awwam da Asma’u ‘yar Abubakar, da suka kulla wannan auren aka sami dansa Abdullah, wannan lamarin kuwa dan Abbas ya gaya wa Abdullah dan Zubair shi yayin da suka yi jayayya, dan Zubair ya haramta bisa umarnin Umar, sai dan Abbas ya ce masa: Je ka tambayi uwarka idan haramun ne.

Domin idan mun duba zamu ga halaccinta lokacin Manzo (s.a.w) da kuma lokacin halifan farko, da wani bangare na lokacin halifancin halifa Umar, har sai da halifa na biyu Umar dan Khaddabi ya fadi mash'huriyar kalmarsa da yake cewa: "Mutu'a biyu (wato auren mutu'a da hajjin tamattu'i) sun kasance a lokacin Annabi (s.a.w) amma ni na hana su, kuma zan yi ukuba (ladabi) a kan yin su"[8]. A fili yake gun musulmi cewa; Umar shi ne farkon wanda ya haramta. Duba Tarihul Khulafa na Suyudi, yayin da ya sanya Umar cewa shi ne farkon wanda ya haramta auren mutu'a. Tarihul Khulafa: 137.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next