Aure Mai Iyaka



Wadannan dukkaninsu sun tafi akan halarcin auren mtutu'a suna masu dogara da wannan ayar, har wasunsu ma sun kara kalmar "zuwa wani lokaci" a gaban wannan ayar kamar haka:

 ÙÙ…ا استمتعتم به منهنّ إلى أجل فآتوهنّ أجورهنّ، "إلى أجل" Domin su nuna ma'anarta da tafsirinta cewa game da auren mutu'a ne.

Abdullahi dan Abbas ya kasance yana rantsewa cewa wannan aya ta sauka game da mutu'a ne. mai son karin bayani yana iya duba tafsirin:

Dabari, da Kurdabi, da Ibn Kasir, da Kasshaf, da Durrul mansur, da Ahkamul Kur'ani na Jassas[11], da Sunan Baihaki[12], da sharhin Nawawi na Muslim[13], da Mugni na Ibn Kuddama[14]. Kuma ana iya duba: Ahkamul Kur'an na Jassas: 2/147, Sunanul Kubura: 7/205, Almugni fil fikhil Hanafi: 7/571, Al'jami'u li Ahakamil Kur'an: 5/130.

Dalili Daga Sunna

Akwai ruwayar da ta zo a Hadisin Annabi (s.a.w) da take nuna halarcin auren mutu'a kamar haka:

Daga Abdullahi dan Mas'ud ya ce: Mun kasance muna yaki tare da manzon Allah (s.a.w) ba mu da mata tare da mu, sai muka ce: Ko zamu fidiye kawukanmu! Sai ya hana mu wannan, sannan sai ya yi mana rangwame da mu yi aure da mace da (sadakin) tufafi zuwa wani lokaci, sannan sai ya karanta wannan ayar a karshen maganarsa kamar haka:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تُحَرِّمُوا طَيِّبَاتِ مَا أَحَلَّ اللهُ لَكُمْ وَلاَ تَعْتَدُوا إِنَّ اللهَ لاَ يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ

"Wato: Ya ku wadanda kuka yi imani, kada ku haramta dadadan abin da Allah ya halatta muku, kuma kada ku yi shisshigi, Allah ba ya son masu shisshigi"[15].

Kuma nufinsa da karanta wannan ayar saboda haramcin da aka yi lokacin halifa na biyu ne. Sannan sai Adiyya ya shiga bayanin hukunce-hukuncen wannan aure. Wannan hadisin ya zo a Kitabun Nikha (wato: Babin Aure) a Sahihul Buhari, da Kitabun Nikha a littafin Muslim, da Kitabun Nikha a Masnad Ahmad bin Hambal.

Dalilin Ittifakin Malamai

Amma idan muka duba Ijma'in Malamai (Ittifakin Malamai), babu wani sabani game da halaccin auren mutu'a tsakanin dukkan musulmi. Wannan yana nuna mana akwai dalilai na Kur'ani da Sunna da Ijma'in malamai a kan halaccin auren mutu'a. Kuma ya zo a Masnad Ahmad bn Hambal: 1/402, da Tafsiru Dabari: 5/9, da Aljami'u Li Ahkamil Kur'an: 5/132.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next