Aure Mai Iyaka



Aure yana bayar da damar kusanci tsakanin namiji da mace; sai dai ba shi kadai ne yake bayar da halaccin kusancin ba[3], shari’a ta bayar da damar kusantar abin da namiji ya mallaka na daga mata, shari’a ta kira su “mulku yamin”.

Amma shi aure ya kasu gida biyu ne a shari’ar musulunci madaukakiya, ya hada da Aure maras iyaka[4] da aka fi sani da “Da’imi” da kuma aure mai iyaka da aka fi sani da “Mutu’a”, dukkan wadannan biyun shari’a tana da hikima, kuma an sanya musu sharudda, sannan aka kwadaitar da yin su. Yawancin aure maras iyaka yakan kasance don hada gida da tara iyali, da renonsu, da samar da al’umma ta gari wacce zata gaji na baya.

Amma aure mai iyaka yakan kasance ne domin kariya daga zina, da fadawa cikin haramun; wannan yana da amfani matuka ga mutane mabambanta; muna iya kawo misalin matafiyi, da wanda ya kasa aure, ga shi kuma yana jin tsoron fadawa cikin zina, da maras ikon sama da mata hudu; ga shi kuwa yana iya fadawa fasadi, da sauran misalai masu yawa. Don haka ne imam Ali (a.s) ya ce: “Ba don Umar ya haramta auren mutu’a ba, da babu mai yin zina sai fasiki”[5].

Wannan lamarin kamar yadda yake ga maza, haka nan yake ga mata; sau da yawa macen da ba ta samun aure, sannan tana son kiyaye kanta daga zina da fada wa cikin sabon Allah madaukaki sakamakon ba zata iya kame kanta ba, ko kuma tana cikin yanayin rayuwa a al’ummar da ko dai ta fada wa fasadi, ko kuma ta zabi kiyaye dokar Allah.

Sai dai wannan bayani ne kawai na wasu daga cikin hikimomin aure mai iyaka, amma ba su ne kawai dalilan sanya shi a shari’a ba, domin akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu. Allah yana da hikimomin da yakan sanya shi zartar da hukunce-hukuncensa, muna iya fahimtar wasu wasu kuwa ba ma iyawa.

Mutu'a a Musulunci

Dukkan musulmi sun yi ittifaki[6] a kan cewa auren mutu'a halal ne a farkon musulunci, kuma sahabbai sun aikata shi a lokacin Annabi (s.a.w) da lokacin halifansa na farko, da wani bangare na shugabancin Umar bn Khaddabi, sannan sai Umar ya hana. Har ma daga baya wasu suka yi da'awar an shafe shi. Amma sahabbai masu yawa sun saba wa Umar kan wannan hanawa da yi, wasu kuma suka goyi bayansa, wasu suka yi shuru.

Amma Ahlul Baiti (a.s) duk sun tafi a kan halarcinsa da hadisai da suka kai matsayin tawaturanci (masu yawa) kuma ga shi Kur'ani yana goyon bayan halarcinsa har zuwa yau.

Da akwai mas'aloli da yawa da duniyar musulmi ta shagaltu da sabani game da su, irin wadannan mas'aloli sun hada da kamar magana kan farkon wanda ya musulunta, da shafa kan kafafu a alwala, da ayyana halifa ta bangaren Annabi (s.a.w), da auren mutu'a.

Sau da yawa irin wadannan mas'aloli a zahiri koda sun shafi mas'alar fikihu ne, amma daga karshe wasunsu sukan tuke zuwa ga Akida ne.

Wani abu kuma da zamu sani shi ne: Sau da yawa masu kare auren mutu'a da dukkan karfinsu ba don su suna son yin mutu'ar ba ne, ko wani abu makamancin haka, abin da yake nufinsu shi ne kare addinin Allah daga jirkita domin maslaha tana cikinsa. Don haka ba ya kan wani mutum ya tambaya cewa: Me ya sa kuke kare auren mutu'a alhalin yawancinku ko kuma malamanku ba sa muhimmanta da yin sa?!



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next