Aure Mai Iyaka



Wannan haramcin na Umar hatta da dansa Abdullahi dan Umar bai yarda da shi ba, yana mai kafa hujja da cewa; hanin Umar ba ya rushe umarnin Annabi (s.a.w). Da wannan ne zamu ga cewa; dukkan al'umma sun yi ittifaki a kan cewa; Umar ya haramta, sai dai wasu don su gyara abin sun so su mayar da hanin zuwa ga lokacin manzon Allah (s.a.w) sai suka fada cikin rudewa kamar yadda zamu gani.

Wanda ya haramta wato: Umar dan Khaddabi ya fadi cewa; Mutu'a ta kasance a lokacin Annabi (s.a.w) amma shi ya hana, sai ya yi nuni da cewa; akwai auren a lokacin Annabi (s.a.w) amma shi yanzu ya hana. Kuma an yi tawiloli kan dalilin da ya sa ya hana, sai dai wannan ba ya kore cewa; shi ne ya haramta. Don haka mutu'a hukuncin musulunci ne da yake nan daram har alkiyama ta tashi, kuma babu wani lokaci da zai zo ba ta kasance daya daga cikin hukuncin shari'a ba wanda yake da amfani mai matukar yawa ga al'umma.

Mutu'a ba zata gushe ba tana nan a matsayin hanyar warware matsalolin yammacin duniya, da latin Amurka, da Afrika da sauran nahiyoyi gaba daya, ba zata gushe ba a matsayin hanyar warwarar matsalolin al’umma da nisantar zina, ko kuma a lokacin tafiya da cakude, ko a matsalolin gidan samari, ko gidajen haya da za a iya auren 'ya'yan juna don ya halatta cakuduwar zaman tare.

Mutu'a zata iya warware matsalar fasikanci ga dalibai a jami’a da cakuduwa da zaurawa da 'yan mata, da takan kai su ga lalacewa, kuma tana iya daidaita sahun karuwai da suka saba mu'amala da mazaje daban-daban ba zasu iya aure maras iyaka ba. Hada da matsalar mutanen da suke tsayawa titina don su samu wanda zai dauke su; irin wadannan mutanen suna iya samun masu shiryar da su domin su daina shashanci su kama hanyar shiriya.

Wani yana iya cewa; mutu'a tana da dokokin shari'a, shin  da wannan lamarin da muka lissafa zai yiwu a kiyaye wadannan dokokin kuwa? Amsarmu a nan ita ce E. Zai yiwu a kiyaye dokokinta, matakin farko dole ne mutane su san cewa; addini ne, sannan kuma a sanar da mutane dokokinta domin su kiyaye, sannan kuma su sani cewa auren mutu'a aure ne fa suke yi ba shashanci ba, don haka dole ne su kiyaye kimar lamarin aure.

Aure ne mai daraja kamar sauran aure, don haka da da za a iya samu dansu ne, sai dai bambancinsa da aure maras iyaka ya shafi abubuwa ne kamar; gado, da wajabcin ciyarwa, da kwana, da sauransu, wannan lamarin ne ma ya sanya shi kasancewa mai sauki matuka, kuma wannan ne ma ya sanya shari'a ta kira shi da auren "Mutu'a", mutu'a a larabci tana nufin "Jin dadi".

Idan Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ba don Umar ya haramta auren Mutu'a ba, da babu wanda zai yi zina sai fasiki". Ina iya ce mana haka yake: Da ba don an yi wurgi da Nasihohin Ayatul-Lahi Dalikani, da Shahid Mudahhari a jamhuriyar Musulunci ba, da babu wanda zai yi zina a kasar sai fasiki. Shin a cikin al'ummarka akwai wanda ya taba tunanin yadda za a warware matsalar saduwa ta barkatai, da warware matsalar mata masu zaman kansu, da masu jin tsoron zina kuma sun rasa mai aurensu, da masu istimna'i (jawo mani da fitar da shi da hannunsu ko wani abu da kansu) har rayuwarsu ta lalace gaba daya, da matsalolin cakuduwa da juna, da ma masu shirin fina-finai (fila-filai) musamman da yake ga mai auren mutu'a akwai saukin dokokin fita. Hada da mazajen da matansu suke tura su gun matan banza saboda mummunan hali da suke musu, ko nushuzi[9] (kin miji a shimfida).

 Sai dai kada mu manta a auren mutu'a ba dole ba ne a sadu, don ana iya shardanta masa rashin saduwa, ana iya yin sa misali don zama tare a mota a tafiya har a isa inda za a rabu, ko don a hada wasu don yin fina-finai kawai, ko zama a wurin kallon cinima, da makamancinsu.

Dalilan Halarcin Auren Mutu'a

Dalilan Kur'ani

Ayar nan ta: فَمَا اسْتَمْتَعْتُم بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً[10] “Abin da kuka ji dadi da shi daga garesu, to ku ba su ladansu bisa wajibi”

Wannan aya tana nuna dalilin halarcin auren mutu'a, kuma akwai manyan sahabbai da manyan malamai da suka tafi a kan haka: kamar Imam Ali (a.s) da Abdullah dan Mas'ud, da Ubayyu dan Ka'ab, kuma wadannan su ne madogara wajan fahimtar ma'anar Kur'ani gun Sunna da Shi'a. Daga cikin tabi'ai akwai irinsu: Sa'id bn Jubair, da Mujahid, da Katada, da Saddiyyi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next