Auren Mace Fiye Da Daya



Wani abin takaici a wasu kasashen na yamma saboda wahala ta dokar mazhabar Addininsu na haramcin saki, sai ka ga kowanne ya kama gabansa shi ke nan, ya je ya nemi wani daban. Muna iya gani a wannan jadawalin babu wata kasa da take ana auran mace sama da daya, sannan kuma Kasar musulmi daya ce a ciki da ta zo ta tara, da wata kuma da ta zo ta sha uku. Sannan kuma a wannan kasashe na masu sukan mace takan zama mai miji amma tana neman wasu, haka ma mijin yana da mace amma yana da mata masu yawan gaske da yake mu’amala da su, amma irin wadannan mutane suna da bakin magana suna sukan musulunci wai yana halatta yin auren mace sama da daya.

Sannan kuma a ina ne aka fi kashe-kashe marasa dalili a duniya da ya kai irin na kasashen yamma, nemi wanda ya je wadannan kasashe ka sha labari, yi bincike kan adadin fyade a duniya ka ga a wasu kasashen duk ‘yan mintina ana yi wa mace fyade a duniyar yamma, Ashe kenan matsalar ba don auren mace sama da daya ba ne. A Amurka a rahoton FBI ya tabbata cewa; a kowane minti 22 ana kisa, a kowane minti 5 ana fyade, a kowane sakan 49 ana sata, a kowane sakan 30 ana kai hari da makami, a kowane sakan 10 ana fashi[15].

Masu Mace Sama Da Daya ‘Yan Kadan Ne

Mutum nawa ne a aikace suke da mace fiye da daya a cikin musulmi, idan muka duba sosai a kasashen musulmi zamu samu cewa; wadanda suke da mace sama da daya idan an kwatantansu da masu mace daya ba su kai ishirin cikin dari ba, wannan kuwa yana nuna nisan tazarar da take tsakanin wannan adadi guda biyu.

Sannan kada mu manta cewa; auren mace fiye da daya bai kebanta da musulmi ba, akwai ma’abota addinai da al’adu masu yawa a duniya da wannan ya kasance daya daga al’adunsu, babban misali kamar tsofaffin addinan kabilun Amurka na farko.

Sukan Yana Hawa Kan Musulmi Ne

Idan ma abin da kuka ce gaskiya ne to sukanku yana hawan kan musulmi ne ba kan musulunci ba, domin da an kiyaye musuluncin da musulmi ba su fada irin wannan balao’i ba. Musulunci ya sanya doka ne da ka’ida, ya dora hukunci da sharudda, kuma ya wajabta yin aiki da su a kan mutane, amma idan mutane ba su kiyaye ba to wannan ba ya zama laifin shi musuluncin.

 Alal misali, mutumin da ba zai iya kiyaye adalci tsakanin matansa na aure ba amma sai ya auri sama da mace daya kuma matsaloli masu yawa suka babaye gidansa, wannan matsala ba ta musulunci ba ce ta shi mai sabawa dokar ne. idan da zai kiyaye dokar da ba zai fuskanci irin wadannan matsaloli da sakamakon ayyukansa suka haifar da su ba.

Misali Na Daya; Cewa Sukan Bai Shafi Addini Ba: Da wani musulmi zai yi kuskure to bai kamata a jingina shi da Addini ba, irin wannan ya faru a wata kasa da malman Addini suka nemi zuwa gaisuwa gidan gwamnatinsu da kuma bayar da shawara a kasar, da suka je gidan gwamnati sai Gwamnan ya turo sakatare aka kawo musu abinci na romon kai da gasasshen ragon barka da salla, sai suka shiga cin abinci har ruwan naman yana biyo hannunsu, ga shi kuwa ana nunawa duniya tana kallo, suka yi godiya aka cika musu aljifansu.

Amma wasunsu da suka kai masa ziyara ba su yarda da ganin sakatare ba sai dai gwamnan, bayan sun zo sai aka nuna musu nasu romon Sai suka ce: Ai ko kadan ba zasu ci ba domin ai kudin talakawa ne ga samari ba aiki, sai nasiha suka yi wa gwamna suka koma.

A nan ne mai bayar da labarin wannan abin takaici ya ce: Ba domin shi musulmi suka haife shi ba a wancan lokaci da ya bar addinin saboda tasirin abin a cikin samarin kasarsu na wannan abin takaici da suka gani. Amma abin da ya kamata ya yi tunani a nan shi ne ba a auna addini da aikin ma’abotansa, don haka addini daban mutanen da suke riko da shi da aikinsu daban. Irin wadannan mutanen da suka rayu cikin kaskanci sai al’umma ta ci ta rage ta ba su suna ganin kansu kaskantattu yaya ko zaka ga sun shiryar da al’umma, duba ka ga yaddda ake mu’amala da su, duk wani abu da ya lalace su ake ba wa.

Yaya kake gani wannan in ya zama wani abu ya je gidan gwamnati, shi yana ganin ya zo bara ne, saboda haka ko nasiha bai iya yi sai dai ya yi addu’a, a ba shi na cin kashi ya yi godiya yana ganin kwarjini. Irin wadannan mutane daidai ne daga cikinsu suke iya tsira sakamakon irin yanayi da suka tashi a cikinsa, a nan kuwa duk da laifi ne na wasu malamai na Addini amma ba ka isa ka jingina shi da Addini ba, domin babu wani Addini da ya fi musulunci izza da daukaka, da rashin rusunawa ga rashin gaskiya, da neman fadin gaskiya komai dacinta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next