Auren Mace Fiye Da Daya



Kasashen musulmi duk da suna da addini daya amma al’adu sun bambanta su, wani misali shi ne a a Gabas Ta Tsakiya saurayi yana iya rike hannun matarsa suna yawo amma a kasar Hausa sai su ga wannan bai dace ba. Haka nan ya kasance da wata daliba yayin da ta ce da ni: Zo mu shiga motar babana. Sai na ga abin mamaki yaya za ta kira ni zuwa motar babanta, Sai ta ce: Ba komai zo mu tafi. Yayin da muka shiga motar Sai babanta ya ce: Ustaz wannan ‘yata ce abokiyar cinikayyata a lokaci guda, a yanzu haka na bude mata ofishin hada cinikayya tsakanin kampanoni, kuma na ba ta shi, kuma ni nake kula da ofishin amma ina da nawa aiki da yamma, da safe ina tsaron ofishin ne a matsayin yaronta: Kwatanta wannan maganganu a mahangar al’adun inda kake.

Bayan al’ada da tasirinta dole ku fahimci cewa daidaikun mutane ma kowannensu yana da mahangarsa game da mace da ta bambanta da ta wani, domin kallon daidaikun mutane ga mace ya sassaba, sai dai abin da nake iya yi wa mata nasiha shi ne; su nisanci auren namijin da yake ganinsu kamar kifi a ruwa da zai sa ‘yar tana da dan abin duniya domin ya kama su da shi. Irin wadannan mazaje ba su cancanci zama magidantanku ba, kuma kada ku sake duniya ta rufe muku ido, abin da ya kamata ku duba shi ne cikar kamala da hankali na mijin aurenku.

Misali Na Biyu: A kasarmu Akidar kaddara ta yi zurfi a imanin mutanenmu wannan al’amarin ya sanya amfani da kalmar kaddara hatta a son rai da gyara barna, ta yadda duk wani abu da zai faru sai a ce kaddara ce, amma da wani zai mari mai wannan hali a misali da ba zai ce kaddara ba ce sai ya nemi ramawa. Amma a sani ba mai musun kaddarawar Allah, sai dai akwai sabani kan menene hakikaninta. Mun sani cewa Allah shi ya halicci komai amma ya halicci komai ne tare da zabisa, don haka idan mutum ya yi sabo shi ne ya yi sabon ba Allah ba.

Shi ya sa kai ba kamar remote ba ne a hannunsa ta bangaren ayyukanka, kana iya sabo kana iya barinsa da ikon da shi ya ba ka, don haka yana iya azabtar da kai idan ka saba. Amma da kamar remote ne kai a hannusa kamar yadda al’ummar kasarmu ta yi imani da hakan, sai ya azabtar da kai a nan da aikinsa ya siffantu da zalunci domin bai ba ka ikon komai ba ko nufi. Amma wannan ba daidai ba ne a fahimtar wasu kasashen musulmi, su suna da fahimtar da muka kawo a farko ne, don haka ne a komai suke tashi su nemi ‘yancinsu.

Ta haka zaka ga al’ummar musulmi daya ce a duniya amma al’adu da mazhabobi sun yi tasiri a ayyukansu, wannan kuma ba matsalar musulunci ba ce matsalar su musulmin ne.

Raddin Sukan Yawan Matan Annabi (S.A.W)[23]

Amma sukan da kuka yi kan yawan matan Manzo (S.A.W) zaku samu raddi mai kaushi daga alkalami mai raddi da taimakon Allah (S.W.T). Ku kun ce: Yawan matan ko ya zama don sha’awa ko don son su.

Sai na ce da ku: Amma son mata ba aibi ba ne, al’amarin son mata ga namiji yana daga cikin kamala da cika da daukaka ne, domin wanda ba ya son su to lallai akwai nau’in tawaya ko na ruhi ko na jiki ko kuma na tunani da yake tare da shi ne, kamar yadda sha’awa ita ma ba aibi ba ce, ita nau’i ce ta halittar Allah da ya yi wa dan Adam.

Sannan kuma aure domin sha’awa wani abu ne mai wuyar ganewa domin yana bukatar ka san mai auren da dalilinsa na yin auren. Da wani zai yi aure da ba wani da ya isa ya danganta shi da sha’awa, aure yana kasancewa ne domin kame kai da ku ba kwa so ya kasance, Sannan kuma yawanci irin wannan yana bukatar budurwa ne da shi mai auren zata iya dauke masa kewar sha’awar tasa, amma mace da ta manyanta ba ka safai ta ke iya wasanni na budurwa da ango ba musamman idan ta bayar da shekaru masu yawa ga mijin.

Amma abin sani game da Manzo (S.A.W), ya auri mata daya ne da ya rayu da ita yana shekara ashirin da biyar tana da arba’in, ka ga kenan da don sha’awa ne da bai auren wacce take da tazara da shi a shekaru masu yawa haka ba, kuma da bai rayu da mata daya har kusan karshen rayuwarsa. Haka ya zauna (S.A.W) da mace daya, sannan a wannan zaman shekara ishirin da biyar ya yi da ita bai sake aure ba yana ta ibada da tunanin fitar da al’umma daga kangin bautar mutum zuwa ‘yanci na bautar Allah.

Bai auri ta biyu ba sai bayan yana dan shekara hamsin da uku ya manyanta, idan dai ba neman sukan fiyayyen halitta da kuke da shi ba wani irin rashin hankali ne zai kawo batun sha’awa a wannan hali da ya fara kira yana cikin takurawa da sanya masa takunkumi da yake-yake, ga shi kuwa kowane wata ana kawo masa hari, ga Kafiran Kuraish, ga na Jazira, ga munafukan cikin gida, ga Rum, ga Farisa, ga Yahudawan jazira da madina da khaibar, ga kiristocin yaman, ga sallar dare wajibi ce a kansa, ga azumi a kansa, ga shiryarwa da koyarwa ga duniya, da abubuwa masu yawa da ba za su kirgu ba. Da sha’awa ce ta sanya yin auren da bai auri masu shekaru da suka manyanta ko suka tsufa ba, ku duba shekarunsu mana ba ‘yan mata ba ne. Duba ku ga Ummu Salama ta haura hamsin haka ma Zainab ‘yar Jahsh.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next