Auren Mace Fiye Da Daya



Kuma su ne suke alfahari da aurensa, har ma an ba su zabi cewa suna iya barinsa in sun so amma suka zabe shi[24]. Sannan kuma yawanci aurensu ya kasance da manufa ne na cimma hadafin musulunci kamar kira zuwa gareshi ko shiryar da wata al’umma. Wata kuwa mijinta ya yi shahada kuma ga ta da ‘ya’ya masu yawa kuma ba mai kula da su ko mai renonsu, ko don karfafa Musulunci, ko don sun bayar da kansu ga Annabi shi kuma ba ya iya kin karbar su.

Duba matar da ya aura Sauda wannan ya kasance don an kashe mijinta a Uhud ne wato Abdullahi Dan Jahsh, kuma tana da alheri har ma ana cewa da ita uwar miskinai saboda alheri da tausayi, sai ya aure ta don ya debe mata kewar rashinsa. Haka ma Ummu Salama mumina mai ibada da tunani mijinta ya mutu tana tsohuwa ga ‘ya’ya da yawa, ga Safiya da an kashe mijinta ne a Yakin Khaibar, don haka Manzo ya sadarda zumuncinsa da ‘Ya’yan Isra’ila, haka ma auransa da Zuwaira ya sa musulmi sun ‘yanta mutanenta, Maimuna kuwa ta bayar da kanta ga Annabi ne, ga Ramla ya aure ta don dakewarta a kan musulunci bayan mijita ya zama Kirista a Habasha lokacin da suka yi hijira zuwa can, kuma ya auri Hafsa ne saboda an kashe mijinta a Badar, ga A’isha ya aure ta budurwa, wannan dalilai ne a kan sabanin da’awar ‘ya’yan Jahiliyyar yamma a kansa mai tsira da aminci

Amma sukan da kuke yi game da yawansu wannan wani abu ne da Allah ya kebance shi da shi kamar yadda ya kebance shi da wajabcin sallar dare, da annabta, da wahayi, da fara kai hari, da azumin wisali, da kai hari Makka sau daya. Shi ya sa a wancan lokacin hatta da makiyansa ba su taba sukan sa da auran mata da yawa ba, domin duk wanda ya yi haka ba mai yarda da maganarsa kamar yadda shi mutumin yamma yanzu da ya ke har yanzu bai waye ba yake wannan sukan yana jingina tawaya ga fiyayyen halitta. Ayanzu ku baku san cewa akwai abubuwa da su ka kebanta da Isa (A.S) ba a zamaninsa, misali wa ke raya matacce ko warkar da marasa gani? Sannan duk kisan da ake yi ba wanda aka dauka sama sai shi? saboda haka Allah ya kebance Annabinsa da wasu dokoki ba laifi ba ne kuma ba aibu ba ne.

Daukaka sha’anin mata yana daga cikin abin da zamu iya fahimta a wannan auren nasu da shi (S.A.W) domin aurensa da ya daukaka sha’aninsu kuma ya nuna wa duniya cewa; da su ne komai zai iya ci gaba, kuma da su ne ya kamata a tafi kafada da kafada kamar yadda yake a tarihin dan Adam da ci gabansa. Sabaninku da kuka mayar da mace kamar abin wasa da kowa sai ya dauka don cimma burinsa na rayuwa kamar yadda ake kama kifaye a ruwa da ‘yar fatsa da koma domin cimma burinn rayuwar Duniya.

Don me ya sa ba mu ga kuna suka kan wani Addini ba sai na musulunci? Ko don hassada da kuke masa cewa Addini ne cikakke kuma fiyayye daga kowanne mai kunshe da dukkan dokoki da tsari kammalalle. Ina tuna wata rana Malama Nasirin ta taba tambaya cewa: Yaya zata iya bayar da amsa a makarantarsu a London? Da a kan nuna masu musulunci kamar cibayayyen Addini musamman misalin mata a kasa kamar Afganistan? Sai na ce da ita: Ta yi kokari ta nuna musulunci daban aiki ko fahimtar musulmi daban, don su wadannan imma sun hada musulunci da al’adunsu ko kuma sun yi wa musulunci wata fahimta maras kyau saboda haka wannan fahimtarsu ce ba shi ne musulunci ba. Idan kuwa suna nufin hijabi na mata shi ma fahinta ce da kowa ya ikance shi bisa mahangarsa, amma idan suna nufin rufe tsaraici ne, sai ki ce: Wannan suna bakin ciki ne ga wasu kamammun mata da ba sa ba wani fasiki dama balle ya ga tsaraicinsu kuma fasadi ya yadu a bayan kasa.

Haka nan Musulunci yake kafa dokokinsa bisa masalaha da kuma kare hakkin iradar mutane matukar ba zai bude musu hanya ta fasadi ba wacce ta saba da hadafin halittar dan Adam.

Haka nan da za a kwatanta Musulunci da sauran addinai da ka ga fifikon musulunci sosai a kansu, amma abin takaici shi ne a duniyar musulmi an samu wasu masu tsukakken tunani da suna kallonsa ta mahanga tsukakkiya sai su nuna shi ga duniya da wata fuska daban. Saudayawa irin wannan al’amarin yakan jawo suka kansa har ya sanya makiyansa su rika yi masa wani kallo da ya sabawa hakikaninsa.

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai

Masdarorin Madogarar Wannan Littafin:

Kur’ani mai girma

Tafsirul mizan



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next