Auren Mace Fiye Da Daya



Don haka mai auren da’imi da yake matafiyi idan  ya yi tafiya sai ya yi zina ba ya cikin muhsinai, haka ma mai auren mutu’a ba tare da yana da da’imin aure ba shi ma ba muhsini ba ne. Da za a kashe wannan ba bisa dokar musulunci ba da laifin ya hau kan musulmi ne da suka bar kofar Ilimin Manzonsu (A.S) imam Ali da Ahlul Bait (A.S) suka bi ijtihadodi da suke cike da sabani. Da sun bi kofar da aka ce musu da ba a samu wannan kuskure mai girma ba, kuma da an samu tsari da ba misalinsa a duniya.

  Misali Na Biyar: Da mata zata ki dafa abinci sai miji ya doke ta, ko ya sake ta, ko rayuwa ta yi muni a tsakaninsu, da ba laifin musulunci ba ne don Musulunci bai shar’anta duka ba a nan, kuma bai ce dole sai ta dafa abinci ba wajabci na shari’a, domin dafa abinci hukunci ne wajibi na kyawawan dabi’u, wato saba shi zai kai ga wahala. Kuma yana iya kaiwa ga karancin kauna da soyayya.

Wannan mataki da ya dauka ya saba wa musulunci kuma kuskure ne a shar’ance, kuma tana da ikon bin hakkinta na duka sai in ta yafe masa, da wannan zai jawo wahala tsakaninsu ba laifin musulunci ba ne laifin musulmi ne. Shi ya sa Manzon Rahama (S.A.W) duk aikin gida ya ba fatima (A.S) na waje kuma Imam Ali (A.S) don rayuwa ta yi kyau da tsari.

Don Allah Mu Tsara Al’amuranmu

Kuma yawanci irin wannan yana faruwa ne sakamakon rashin tsara gida da lokuta da kuma ba wa kowa hakkinsa na lokacin aiki da hidimar gida, tsari wani abu ne wanda imam (A.S) ya yi wasiyya da shi ga musulmi gaba daya[22]. Irin wannan ne ya sanya matar gida cikin wahala, ba lokacin karatau, ba na ‘ya’yanta, ba na hutawa, shi kuma mai gida lokacinsa gaba daya na hira ne da abokai da kasuwa sai bacci, amma ‘ya’ya da uwar gida ko kadan ba su da nasu lokaci da za su tattauna da mai gida.

Misali da mai gida zai ware; awa takwas don neman abin rayuwa, awa shida na bacci ne, awa hudu na yara ne, awa biyu na matansa ne, awa biyu na hutawa ne, awa biyu na karatu ne, amma sai ka ga ya ware awa 7 na bacci, awa 10 na kasuwa, awa 7 na hira, shi ke nan duk rayuwa haka za ta tafi. Haka ma uwar gida tana iya tsara nata awoyin; a misali ta ware awa 7 na hira da aikin gida ne, awa 4 na yara ne, awa 2 na mijin ta ne, awa 3 na karatu ne awa 2 na hutawa, awa 6 na bacci ne.

Da haka zai samu da yara sun samu awa takwas, hudu da babansu suna karatu da hira da wasa hudu kuma da babarsu, haka ma mace tana iya dafa abincin dare da na rana da rana, da dare sai ya zama ba abin da ya rage mata sai karatu da kula da na yara, amma rashin tsari sai ya jawo ta rayu cikin wahala ta tsufa ta na jahila har ma wajibi ba ta sani ba.

Wannan ga mai gida ma haka abin yake zama har ma wani jahili ya saki matarsa don ta dafa danwake saboda ya yi baki, kuma a wajansa danwake ba wani abinci ba ne na burgewa, wani kuma yana da jikoki amma ya dauka wankan janaba sai an yi zina ne sannnan ake yinsa. Saboda haka masu suka ku sani duk wannan ba ya komawa ga musulunci yana komawa ga musulmi ne.

Masu Wadannan Soke-soke Sun Rufe Idanuwansu

Abin mamaki shi ne: da kuka rufe idanuwanku game da tarihin musulunci lokacin da ya rike duniya ya wayar muku da kai, ya zo da tsari da babu kamarsa, da adalci da ake buga misali da shi, da tsarin rayuwa mafi kamala a tarihin dan Adam. Domin tsari ne da ba a kwatanta shi ko kusa da Demokradiyya ko Gurguzu. Ba don Yakin Salib da kuka kai shi kan duniyar muslulmi ba kuka samu littattafansu da ba ku gane abubuwa da yawa ba, haka ma Daular Andulus ta wayar da ku kuma duk musulunci ne ya kawo wannan.

Mutanen da kuke wa kirari da mafasarrin ilimi mai girma “Ibn sina” musulmi ne mai biyayya ga Ahlul Bait (A.S), Haka ma “Ibn rushdi” babban malamin Falsafa a Andulus da “Farabi” da “Al-kindi”. Amma sai kuka dauki wanda ya amfani al’adunku a duniya kuka jefar da wanda bai yi muku ba, sannan domin rashin adalci kuna ganin sauran kwakwale na mutanen duniya ba su nuna ba saboda haka ba su isa sha ba, kai ba su ma bura ba suna nan danyu sharaf balle su iya tunani mai zurfi.

Tasirin Al’aduDa Bambancinsu A Tsakanin Musulmi

Misali Na Daya: Ku sani al’adu sukan yi tasiri a kan rayuwar mutane fiye da addini, idan mun duba zamu samu karancin mutanen da suke kiyaye dokokinsa, mafi yawancin mutane suna himmantuwa wajan kiyaye al’adunsu ne, kuma su suka fi yin tasiri a kansu fiye da addininsu. Duba ku ga Farisa da Saudiyya da Misira yadda rayuwar mutane ta saba da ta mutanen Arewacin Nijeriya duk da kuwa dukkansu musulmi ne, shi ya sa kuskure ba daga Addini ba ne daga al’adu da rashin kiyaye Addinin ne. Wannnan ya faru ne a kanku tun bayan Renosans da ya faru a cikinku na juyin juya halin tunani bayan kun gaji da Addini sakamakon zaluncin ma’abotansa a kanku, sai kuka dauka duk laifi daga addini ne maimakon ku mayar da shi kan ma’abotansa da suka hana ilimi ci gaba a cikinku, don haka ku sani musulunci shi ne ya zo da ci gaba da kwadaitarwa kan bincike na ilimi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next