Auren Mace Fiye Da Daya



Amma abin takaici matan ba su ko damuwa ba su jin zafi da zogin abin da yake faruwa a zukatansu, suna ganin mazansu na yin wannan mummunar alfasha amma ba sa damuwa, haka ma namiji yakan san cewar matar da zai aura ta kusanci namiji ba daya ba, ba biyu ba, amma yana alfahari wai zai auri matar da kowa yake so tana da farin jini kuma shi ya ci nasara.

Wani Ba’irake yana cewa: Shi Jamus ya tafi gudun hijira sakamakon kashe muminai da shugaban kasarsu yake yi, ga kudi yana samu amma tsoron kada ‘ya’ya su lalace shi ya sa ya ga gwara ya dawo Farisa ya zauna har Allah ya rusa shugaban kasarsu ya koma gida, domin ya zabi talaucin Farisa a kan ‘ya’yansa su lalace. Duba ka ga al’adun da suke faruwa amma duk ba su ga wannan ba sai musulunci a ke gani da ya sanya dokoki da zasu hana magidanci fita neman matan banza da zinace zinace.

Wannan Al’adunku Ne Ko Kuskure Na Mace

Amma da kuke cewa zata yi daukar fansa ko ta bar aikin gida ya lalace sai in ce: Ku kun dauka ne cewa kowa yadda kuke haka yake, to ku sani akwai bambanci, yawancin ‘yan matan kasarmu kafin su yi aure suna da siffa ta kamewa ne duk da kuwa halittarsu ba ta saba da ta matanku ba.

Haka ma idan sun yi aure suna kiyaye dokoki da Allah (S.W.T) ya gindaya musu na kamewa domin suna da tunanin samuwar Allah da Lahira da Wuta da Aljanna da ya dasu a kwakwalensu, ba suna da tunanin rayuwa daban addini daban ba ne, haka ma ba suna da tunani na dole su kadai ba ne mata a gidajen mazajensu.

 Irin wannan tasiri da al’adu kan yi wa tunani ne Mista Bacon ya yi nuni, Mista Farancis Bacon wanda daya daga malaman Falsafa ne a yamma na farko farkon Renosans wanda yake cewa: Akwai abubuwan da suke hana mutane tunani mai kyau ya kuma ba su suna kamar haka; Gunkin kabila, da na kasuwa, da na tunani, da na kogo, wato wani lokaci al’ada takan iya tasiri a tunani ta hana shi hange mai kyau.

Bari in ba ku misali, matan da ba sa tattalin miji ba sa tsafta, ga kasala, ko kuma wasu marasa haihuwa ne, da kuma maza da ba zasu iya hakura da mace daya ba duk ya za a warware matasalarsu, akwai lokacin da zai zama magance wasu matsaloli shi ne dole namiji ya auri sama da daya.

Koda yake ba ina cewa warwarar kowace matasala shi ne namiji ya kara aure ba ne, domin wasu kan yi wannan kusukure ba tare da koma wa masana kan al’amarin iyali ba, idan ya karo aure idan ba mai zurfin tunani ba ce, sai uwar gidan da take da mataslar da ya sanya ya karo aure musamman idan matsalar ta  sabani ce tsakaninsa da ita, sai ta zuge ta sai su wahalar da mijin, sai ya yi ta uku ita ma haka, sai ta hudu, sai ka ga nan da nan sun tara masa furfura a ka ya tsufa, da irin wadannan mutane zasu samu masana da sun ba su shawara da warwara ga matsalolinsu.

Duniyarku tana da wadancan al’adu ne shi ya sa kuke wannan magana, amma duniyar musulmi ba ta da wannan abu da kuke fada, matsalar matar sarki shi ne ba ta da ido da ta hango abin da ke kanta ina ganin da ba ta yi maganar ba.

Kishiyoyi Da Zabinsu Ne Ba Tilas

Wata amsar ita ce matar da ake aura ta biyu da ta uku da ta hudu duka ba bisa tilas ba ne duk da yardar su ne domin a musulunci auren tilas ba aure ba ne. Don haka kun ga kenan idan kuna yi ne da sunan sukan musulunci ko nemar wa mata ‘yanci na karya to su ba su gode muku ba domin ba da yawun su ba ne, kuma ba tilas aka yi musu ba domin bisa zabin su ne, amma na cikin gida mun riga mun yi bayani cewa su suna da masaniya cewa ba dole ba ne su zama su kadai.

Muhimmi shi ne, ina so in sanar da ku cewa yawanci ba abin da yake sa mace rashin son zama su biyu ko sama da haka sai tunanin cewa idan wata ta zo ba mamaki a wulakanta ta, ba ka safai suke damuwa ba in ba wannan. Bincike ya nuna mafi yawansu abin da suke tsoro ke nan, na’am kana iya samun wasu ciwo ne na kishi maras ma’ana ko ki, amma ma’auni shi ne abin da yawanci suke fada kuma masana suka tabbatar.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next