Addinin Musulunci



Na uku: Akwai mudda da lokaci ga wannan zamani na duniya. Kamar yadda ya zo a Bakara: 36.

Na hudu: Shiriyar Allah ta sauka garesu. Kamar yadda ya zo a Bakara: 38.

Na biyar: Sun shakkala al’umma guda[18]. Kamar yadda ya zo a Bakara: 213. kuma Allah ya aiko annabawansa domin su shiryar da mutane.

2- Marhalar sabani da yaki tsakanin gaskiya da karya

A wannan marhala mutane suka fara taurin kai da shisshigi da zaluntar juna kamar yadda ya zo a Bakara: 213. A wadannan sharuddan ne Allah ya aiko annabawa da shiriya da hukunci tsakanin mutane kamar yadda ya zo a Bakara: 213. Muminai daga cikinsu suka karbi shiriya, yayin da sauran suka kafirce mata.

 A nan ne faruwar gaba da yaki tsakanin gaskiya da karya ya fara, kuma a wannan marhalar ce mutane suka shiga cikin sunnar Allah gamammiya da kebantacciya kamar yadda muka yi bayaninsu a baya. Sai aka samu yanayin kama-ka-ba-ni tsakanin bata da shiriya, wannan ya zo ya kawar da wancan, wancan ya zo ya kawar da wannna. Kamar yadda ya zo a Ali Imran: 140 – 141.

Wannan asakala ta faru ne ta hanyar wani lokaci; barna da bata da zalunci da jirkita addini da girman kai su yi nasarar kafa hukuma na wani dan lokaci[19], wani lokaci kuwa gaskiya da shiriya da salihanci su dawo su kafa addini na gari[20].

Duk sadda aka kafa hukumar gaskiya to mutane suna fadawa cikin sunnar Allah ta jarrabawa, idan suka ci wannan jarabawa sai hukumar gaskiya ta ci gaba, amma idan suka kasa cin jarabawa suka yi sako-sako da gudanar da dokokin Allah sai dawagitai su samu damar shugabanci, tun da sunnar Allah ba ta canzawa sai a samu rushewar al’umma. Haka nan wannan hawa da sauka zai ci gaba har a samu cin nasara da galabar gaskiya a karshen duniya.

3- Marhalar karshen zamani da cin nasarar gaskiya

A wannan marhalar ce mutane da kansu zasu samu canji a ransu, su nemi rushe asasin barna tun daga asasi, a samu dawwamar hukumar gaskiya: “Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Ra’adi: 11. Sai Allah ya aiko musu da mataimaki daga gareshi, “... ka sanya mana mataimaki daga gareka…”Nisa’I: 75.

A kan wannan sharadi ne Allah zai aiko da taimakonsa bisa sunnarsa ga mutanen sai barna da bata su kau, “domin bata ya kasance mai gushewa ne”. Isra’i: 81. Sai addinin musulunci ya yi galaba a kan dukkan wani addini. “… domin ya dora shi a kan addini dukkaninsa”. Saff: 9.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next