Addinin Musulunci



Ta biyu: Kebantacciyar sunna ko sunna mai dabaibayi

Wannan ita ce sunnar da aka yi mata sharadi da zabin mutane game da zabar hanyar gaskiya ko bata, a nan mutane sun kasu gida biyu, ma’abota tafarkin gaskiya da shiriya da ma’abota tafarkin karya da bata.

Wadanda suka bi hanyar gaskiya da shiriya su suna da dadin ni’imar duniya da lahira, da kawata musu imani, da cin nasara kan makiya, yana daga abin da ayoyi masu yawa suka yi magana a kansa[15].

Wadanda suka bi hanyar karya da bata suna da dadin bata da kawata musu ayyukansu, da yi musu kofar rago, da rushewa a gaban makiyansu, da bala’in musifu, al’amarin da ayoyi masu yawa suka yi magana game da shi[16].

Domin fahimtar wannan nazari na musulunci sosai dole ne mu kawo mahangar da ta zo a cikin ayoyi game da halittar mutum da marhalolin da ya wuce na tarihi. A bisa wannan mahanga akwai daura biyu na asasi na tarihi ga dan Adam.

Zaman aljanna da sauka kasa

Zaman aljanna[17] lokaci ne da Allah ya halicci Adam da Hawwa a cikinsa, a wannan lokaci akwai yalwa da walwala da ni’ima da farin ciki, da gaskiya.

Lokacin sauka kasa shi kuwa lokaci ne da ya biyo bayan barin Adam da Hawwa aljanna zuwa duniya sakamakon waswasi da shaidan ya yi musu, wannan lokaci shi kansa ya kasu kashi uku:

1- Marahalar sauka da kafa al’umma daya

Bayan Adam da Hawwa sun saba sai aka fitar da su daga aljanna, kuma suka zauna a duniya domin su tuba, wannan saukar ta faru ne a yayin da:

Na daya: Wasu daga cikinsu suna gaba da wasu ne. Kamar yadda ya zo a Bakara: 36.

Na biyu: Dukkansu wato Adam da Hawwa da shaidan sun sauka kasa gaba daya. Kamar yadda ya zo a Bakara: 38.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next