Addinin Musulunci



“Hakika akwai abin lura ga masu hankali a cikin kissarsu”. Yusuf: 111.

“Lallai a cikin hakan akwai abin lura ga wanda yake jin tsoro”.  Nazi’ati: 26.

Haka nan yake kawo bayani game da alakar zalunci da abin da yake sabbabawa na halakar da mutane, da kuma tsoron Allah da abin da yake kawowa na samuwar albarkar sama da kasa… sannan ya kawo sakamakon mutanen annabi Musa da Ibrahim da Nuhu da Adawa da Samudawa da Ludu da Shu’aib (A.S). Kuma ya yi nuni da tarayyar al’ummu a hukunci iri daya game da dokokin zamantakewar al’umma, da na kyawawan dabi’u, da tsarin dokar shari’a, da na al’adu[14]. Sunnar Allah a cikin al’umu ta kasu kashi biyu:

Ta daya – Gamammiyar sunna ko sakakkiyar sunna

Wannan ita ce sunnar Allah a cikin al’umma da kuma a kan daidaikun mutane da ta hada da:

1- Sunnar shiryarwa ta hannun annabawa

2- Sunnar jarrabawa

3- Sunnar taimakon Allah ga dukkan halitta

Kamar ayar da take cewa: “Ubangijinmu wannan da ya ba wa kowane abu halittarsa sannan ya shiryar (da shi)”. Daha: 50.

Amma ayar jarrabawa kamar ayar nan da take cewa: “Tabbas hakika sai mun jarrabe ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawayar dukiya da rayuka da ‘ya’yan itace”. Bakara: 155.

Da kuma ayar da take nuna sunna ta uku kamar: “Wanda yake son rabon lahira zamu dada masa daga rabonta, wanda yake son rabon duniya zamu ba shi daga gareta amma a lahira ba shi da wani rabo”. Shura: 20.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next