Addinin Musulunci



1- Shi ne wanda ya aiko manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya dora shi a kan addini dukkaninsa koda mushirikai sun ki. Tauba: 33. da Saff: 9.

2- Hakika mun rubuta a cikin zabura bayan Ambato cewa; kasa bayina na gari ne zasu gaje ta. Anbiya: 105.

3- Kuma muna son mu yi baiwa ga wadannan da aka raunatar a bayan kasa mu sanya su shugabanni kuma mu sanya su masu gadewa. Kasasi: 5.

4- Musa ya ce da mutanensa ku nemi taimako da Allah kuma ku yi hakuri, hakika duniya bayin Allah na gari ne zasu gaje ta. Kasas: 5.

5- Allah ya yi alkawari ga wadannan da suka yi imani suka yi aiki na gari zai maye su a bayan kasa kamar yadda ya maye wa wadanda suke gabaninsu… Nur: 55.

Kur’ani ya yi magana game da wannan al’amari a sama da aya dari da ishirin…[10]

Ayoyin da aka yi maganar a cikinsu sun hada da; Bakara, Ali Imran, Nisa’i, A’arafi, Nifal, Tauba, Hud, Yusuf, Ibrahimi, Hijir, Isra’i, Maryam, Daha, Anbiya, Hajj, Muminun, Nur, Furkan, Shu’ara’, Namal, Kisas, Rum, Sajadat, Saba’, Saffat, Sad, Zumar, Shura, Zukhruf, Dukhan, Jasiya, Muhamamd, Fath, Kaf, Zariya, Dur, Kamar, Rahaman, Hadid, Mumtahannat, Saffi, Maliki, Ma’arij, Jinn, Mudassir, Takwiri, Inshikak, Buruj, Darik, Gashiya, Fajr, Shams, Lail, Kadar, Bayyaina, da surar Asar.

Allama Hashimi Husaini baharani ya ambaci ayoyi masu yawa a littfinsa “Almahajjatu fi ma nazala fil ka’imil hujja”[11].

A bisa wannan asasin karshen duniya na musulunci ne kuma a wannan babu wani kokwanto:

Na daya: Za a kawar da barna.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next