Addinin Musulunci



Don haka babu wani abu mai suna tilas a tarihi, nufin mutum shi ne yake da tasiri mai girma da muhimmanci wajan ayyana tarihi.

Na biyar; Musulunci yana kore asalin karo da juna a matsayin wani abu mai motsar da tafiyar tarihin dan Adam. Wato yana kore karo da juna tsakanin dabakoki a matsayin mai ayyana tafiyar tarihin dan Adam, maimakon haka yana magana game da karo da juna tsakanin shiriya da bata ne, ko gaskiya da karya[6].

A mahangar musulunci gaskiya da karya a cikin al’mma a kodayaushe suna karo da juna ne, wannan kuwa tun daga farkon lokacin ‘ya’yan annabi Adam (A.S) na farko, rikici ya fara tsakanin bangarori biyu, daya domin biyan sha’awar ransa da jawo wa kansa amfani, da hassada, da son rai, don haka sai ya kashe dayan… wannan rikici yana zuwa a kowane lokaci da yanayi mabanbanci…[7]

Domin tabbatar da abin da aka fada a nan zamu kawo wasu daga ayoyin kur’ani mai girma:


A- Duba Zuwa Ga Tarihi A Dunkule

Kur’ani ya yi magana kan sunnar Allah a tarihi wacce ba ta canjawa ba ta jirkita, kuma rawar da nufi da zabin mutum zasu taka a wannan canje-canje yana iya zama hasashen walwala da sa’adar da zasu samu a karshen zamani.

Littafin Allah a yanke yana tabbatar da cewa nasarar karshe ta addinin musulunci ce, galaba ce ta salihai da masu tsoron Allah da yanke hannun masu barna da jabberai har abada ta hanyar nasarar gaskiya da shiriya a kan karya da barna.

Wannan tunani yana ba mu hasashen mai kyau game da karshen zamani da kore hasahen sharri ga karshen zamani game da rayuwar dan Adam ta karshen duniya[8].

Shahid Mudah’hari yana fada game da karshen zamani a mahangar kur’ani mai girma: “A mahangar kur’ani tun farko yaki ya fara tsakanin jama’ar gaskiya da ta bata. Jama’a ta farko kamar Ibrahim, da Musa, da Isa, da Muhammad, (A.S) da mabiyansu, na biyu kuwa kamar Namarudu, da Fir’auna, da Yahudu da Abu Sufyan da makamantansu… amma mun fahimta daga ruwayoyi cewa karshen yaki shi ne na Mahadi da aka yi alkawarin zuwansa (A.S) …[9]

A mahangar kur’ani karshen zamani na musulunci ne kuma daular musulunci zata kafu a karshen zamani. Ayoyi masu yawa ne suka tabbatar da hakan:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next