Zabar Masoyi (Aboki)



Da kuma ka zo masa kana kiransa zuwa ga mutuwa, da bai

Juyar da kai ba domin (son) wanzuwarka saboda kauna[55].

5 / 10

Mafi Kamalar ‘Yan’uwa

200. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ya kasance ina da wani dan’uwa mai kauna saboda Allah, ya kasance kankantar duniya a idanunsa yana sanya girmama shi a idanuna, kuma ya kasance ya futa daga ribacewar ikon cikinsa (ba ya cin haram), shi ba ya marmarin abin da ba ya samu, kuma ba ya yawaitawa idan ya samu, ya kasance mafi yawancin lokutansa yana mai yin shiru ne, idan kuwa ya yi magana sai ya wuce masu surutu a kayatarwa, kuma ya kashe kishirwar mai tambaya.

Ya kasance mai rauni abin raunatawa, idan kuwa yaki ya zo, to shi ne zakin jeji, kuma kumurcin kwararo, ba ya kawo hujja har sai ya zo wa mai hukunci, kuma ya kasance ba ya zargin wani a kan abin da yake iya samun uzurinsa a irinsa har sai ya ji maganar mai neman uzurin, kuma ya kasance ba ya kai kukan wani zogi sai yayin warkewarsa, kuma ya kasance yana fadar abin da yake aikatawa ne, kuma ba ya fadar abin da ba ya aikatawa, kuma idan an yi galaba a kansa da yawan surutu, to ba kuwa za a yi galaba a kansa ba a kan yin shiru. kuma ya kasance ya fi kwadayin ya ji abin da ake fada fiye da ya yi magana da son rai kuma ya saba. To ku yi riko da wadanna halaye ku lizimce ta, kuma ku yi rige a cikinta, idan kuwa kuka kasa, to ku sani riko da kadan ya fi barin mai yawa[56].

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

hfazah@yahoo.com


[1] Sunan abu dawud: 4, 259, 4833.

[2] Sifatus Shi'a, 84 / 8.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next