Zabar Masoyi (Aboki)



Amma ‘yan’uwan murmushi (na raha da sakin fuska) idan kana iya samun jin dadi daga garesu, to kada ka yanke wannan daga garesu, kuma kada ka nemi wani abu sama da hakan na daga sirrinsu, ka ba su fuska matukar sun ba ka sakin fuska da zakin harshe (dadin baki)[22].

5 / 6

Tsoratarwa daga lalattaccen aboki

Sai mai fada daga cikinsu ya ce: “Ni hakika ya kasance ina da aboki. Yana mai cewa shin kai kana daga msu gaskatawa. Cewa; idan mun mutu mun zama turbaya da kashi shin za a saka mana. Ya ce; shin ku masu tsinkayawa ne. sai ya tsinakaya sai ya gan shi a cikin tsakiyar wuta mai kuna”[23].

“Ranar da azzalumi yake cizon hannunsa yana cewa; kaicona ina ma dai na riki tafarki tare da manzo. Ya kaicona ina ma dai ban riki wane masoyi ba,. Hakika ya batar da ni daga ambato bayan ya zo mini. kuma shedan ya kasance mai halakar da mutum ne”[24].

“Sai wasunsu suka fuskanto ga sashensu suna masu tambaya. Suka ce ku hakika kun kasance kuna zo mana ta dama. Suka ce ba haka ba ne, ku ne dai ba ku kasance maminai ba. Ba mu da wani tilasci a kanku, ku dai kun kasance mutane ne masu dagawa. Sai zancen ubangijnmu ya tabbata a kanmu hakika mu masu dandana azaba ne. sai muka halakar da ku hakika mu mun kasance halakakku ne”[25].

170. Littafin Kafi daga Ali dan asbad daga garesu (A.S): yana daga abin da Allah madaukaki ya yi wa Annabi Isa (A.S) wa’azi da shi: ya kai Isa (A.S)! ka sani cewa ma’abocin munin hali yana tasiri, kuma aboki mai munin hali yana halakarwa. To ka san wanda zaka yi abota da shi, ka kuma zabar wa kanka ‘yan’uwa daga muminai[26].

171. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafi dimautar dimuwa shi ne mummnan aboki[27].

172. Daga gareshi (S.A.W): na hana ka mummunan aboki; hakika shi yanki ne daga wuta, sonsa ba ya amfanarka, kuma ba ya cika maka alkawarinsa[28].

173. Daga gareshi: kadaituwa ta fi mummunan majalisi, kuma majalisi salihi nagari ya fi kadaituwa[29].

174. Imam Ali (A.S) Wanda ‘yan’uwansa (abokansa) suka tabe bai taba rabauta ba[30].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next