Zabar Masoyi (Aboki)



Zabar Masoyi (Aboki)

5 / 1

Muhimmancin Zabar Masoyi

148. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mutum yana kan addinin abokinsa ne, don haka sai dayanku ya duba wa zai abokantaka[1].

150. Imam Ali (A.S) ya ce: zama da ashararai yana kawo mummunan zato ga zababbu, kuma zama da zababu yana sanya lissafa ashararai cikin zababbu, kuma zama da fajirai ga nagari, yana sanya a sanya fajirai cikin nagari, kuma dukkan wanda al’amarin ya rikitar masa kuma ba ku san adininsa ba to ku duba abokan huldarsa idan sun kasance ma’abota addinin Allah ne, to shi ma yana kan addinin Allah ne, idan kuma sun kasance ba a kan addinin Allah ba, to ba shi da wani rabo daga addinin Allah [2].

151. Imam Ali (A.S) ya ce: abokin mutum yana nuna hankalinsa ne[3].

152. Kanzul fawa’idi: An ruwaito daga Sulaiman (A.S) ya ce; kada ku yi wa mutum wani hukunci sai kun kalli wanda yake abokantaka; ku sani ana sanin mutum da ire-irensa ne da abokansa, kuma ana jingina shi da abokansa da ‘yan’uwansa ne[4].

5 / 2

Jarraba Masoya

153. Imam Ali (A.S) ya ce: Ka gabatar da jarrabawa wajen rikon ‘yan’uwa; hakika jarrabawa ma’auni ne da ake rarrabewa tsakanin zababbu da ashararai[5].

154. wanda ya riki dan’uwa bayan kyakkawar jarrabawa to abotakarsa zata dawwama, kuma soyayyarsa zata karfafa[6].

155. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda bai sanya lura wajen zabar ‘yan’uwansa (abokansa) ba, to rudi zai kai shi ga abotakar fajirai[7].

156. Imam Ali (A.S) ya ce: Nutsuwa zuwa ga kowane mutum kafin jarraba shi, gajiyawa ce[8].



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next