Zabar Masoyi (Aboki)



175. Lukman (A.S) yana gaya wa dansa: wanda ya yi abota da mai munin hali ba ya kubuta[31].

5 / 7

Mafi Munin (Sharrin) ‘Yan’uwa

176. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwa shi ne wanda aka dora wa kai nauyi saboda shi[32].

177. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwa shi ne mai sadarwa (makalewa) lokacin yalawa, mai rabuwa (gujewa) lokacin bala’i[33].

178. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; mai yin algush, mai yaudara[34].

178. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; wanda ya yardar da kai da barna[35].

180. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; wanda ya bukatar da kai zuwa ga cakuduwa (fadawa laifi), kuma ya tura ka zuwa ga bayar da uzuri[36].

181. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; wanda ya jinkirtar da kai ga barin alheri, kuma ya jinkirtar da kai tare da shi (ya sanya ka ci baya)[37].

182. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka kuma mafi algush dinsu, shi ne; wanda ya ya yaudare ka da magaggauciya (duniya), ya shagaltar da kai daga majinkirciya (lahira)[38].

5 / 8



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next