Zabar Masoyi (Aboki)



165. Imam Ali (A.S) ya ce: ‘Yan’uwa suna yawaita kwarai yayin kabaki (yalwa), kuma suna yin karanci kwarai yayin musibun zamani[17].

166. Imam Ali (A.S) ya ce: Mafi nisan mutane safara, shi ne; wanda yake safararsa ta kasance domin neman dan’uwa na gari[18].

5 / 5

Nau’o’in Abokai

167. Imam Ali (A.S) ya ce: abokanka su uku ne, makiyanka su uku ne; amma abokanka su ne; abokinka, da abokin abokinka, da makiyin makiyinka. Amma makiyanka su uku ne; makiyinka, da masoyin makiyinka, da kuma abokin makiyinka[19].

168. Tuhaful Ukul: Imam Husain (A.S) ya ce: ‘yan’wa su hudu ne: dan’uwa (amfani) gareka da kuma (amfani) gareshi, da kuma dan’uwa (amfani) gareka, da kuma dan’uwa (nauyi) a kanka, da kuma dan’uwa ba (amfani) gareka ba, ba (amfani) gareshi ba.

Sai aka tambaye shi ma’anar wannan magana sai ya ce: amma dan’uwa gareka da kuma gareshi; shi ne wanda yake neman wanzar da ‘yan’uwantaka da ‘yan’uwantakarsa gareka, kuma ba ya neman kashe ‘yan’uwantakar da ‘yan’uwantakar tasa, to wannan shi ne; dan’uwa gareka da kuma gareshi, domin idan ‘yan’uwantakar ta samu to rayuwarsu su biyu zata yi dadi gaba daya, kuma idan haka ‘yan’uwantakar ta fada cikin lalacewa to sai su rushe gaba daya.

Amma dan’uwan da yake gareka, shi ne dan’uwan da ya fitar da kansa daga cikin kwadayi zuwa ga halin kauna, ba ya kwadayin duniya a cikin ‘yan’uwantakarsa, kuma yana ba ka rayuwarsa gaba daya.

Da kuma dan’uwan da yake (nauyi) a kanka; shi ne wanda yake sauraron duk wata musiba ta fada maka[20], yana boye maka, sirrinsa (da duk wani abu na karuwa da farin ciki), kuma yana yi maka karya tsakanin jama’a, kuma yana kallonka kallon mai hassada (gareka), la’anar Daya (Allah ) ta tabbata a kansa.

Amma dan’uwa ba gareka ba, ba gareshi ba shi ne wanda Allah ya cika masa wauta, to Allah ya nisanta shi, sai ka ga yana nuna son kansa a kanka, kuma yana neman naka yana mai yi maka kauro[21].

168. Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: wani mutum ya zo wajen Imam Ali (A.S) a basara sai ya ce; ya amirul mumini ka ba ni labarin ‘yan’uwa? Sai ya ce; ‘yan’uwan kala biyu ne; ‘yan’uwan aminci da ‘yan’uwan murmushi (na raha da sakin fuska). Da kuma sirri da iyali da dukiya. To idan ka kasance kana da dan’uwa na aminci sai ka ba shi dukiyarka da jikinka, kuma ka so wanda ya so shi, ka ki wanda ya ki shi, ka bayyana masa kyakkyawa. Ka sani ya kai mai tambaya sun fi jan kibrit karanci.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next