Auren Mutu'aMalaman furu'a sun kasu kashi biyu a kan auren mutu'a; akwai wadanda ijtihadinsu ya kai su ga halatta shi (wadannan su ne daukacin malaman Shi'a a jiya da yau, da wasu 'yan tsiraru daga malaman Ahlusunna); sai kuma galibin malaman Ahlussunna, wadanda ijitihadinsu ya kai su ga haramta shi. Amma duk da haka, malaman suna da wasu hukunce hukunce da suka dora mabiyansu a kai; misali mazhabar Malikiyya sun dace a kan cewa: 1. Idan dan Malikiyya ya yi mutu'a a raba auren. 2. Matar da a ka yi mutu'a da ita ta cancanci dukkan sadakin da aka dace idan mijin ya taba saduwa da ita, da rabin sadaki idan bai taba saduwa da ita ba. 3. Kar a yi musu haddi (ba bulala ba balle jifan zawarawa); sai dai wasu sun ce a tsawatar da su da wata ukuba da alkalin shari'a ya ga ta dace. 4. Idan aka sami ciki dan yana bin ubansa ne, kuma dan halal ne. Wannan ne ya sa Mal. Ja'far ya ba ni mamaki yayin da ya ce: "duk dan da aka samu ta auren mutu'a ba dan aure ba ne!" alhali hatta a cikin Iziyya ta Shazili (wanda ake karanta shi daga matakin farko na karatun fikihu a kasar nan) an tabbatar da sabanin haka a Babi na Takwas a kan Aure da Saki (shafi na 201-202), da cikin Thamaruddani sharhin Risala ta Abu Zaid (shafi na 447). 5. Da yana gadon iyayensa bisa fatawarsu ta cewa dan na bin ubansa. Su kuwa 'yan Shi'a da suke halatta shi, suma sun bayyana hukunce hukuncensa; wasu daga cikin wadannan hukunce hukunce sun hada da: 1- Sadaki sharadi ne a cikinsa; yana iya zama duk abin da ma'auratan suka dace a kai. 2- Idan ba a ambaci mudda a lokacin daura shi ya zama na dindindin. 3- Ba a wajabta gado tsakanin ma'aurata a cikinsa ba, sai a inda aka shardanta hakan a lokacin daura shi.
|