Auren Mutu'a



a) Imam Ali bin Abi Talib: a hadisin Abubakr bin Abi Shaiba, wanda isnadinsa ya hadu da Sufyan bin Uyaina daga Zuhri, ya kare da Ali [AS] ta hanyar dansa Muhammad (binl-Hanafiyya), wanda kuma yake cewa (wai Ali) ya ce: "Lallai Manzo (SAWA) ya hana auren mutu'a a lokacin (yakin) Khaibara kuma ya hana cin naman jakunan gida." Wannan ya maimaitu da lafuzza makusanta a kusan duk littafan hadisai na Ahlussunna.

Wannan hadisi ba ya iya zama hujja a kan goge mutu'a saboda dalilai ma su zuwa:

1. Yana da babbar matsala a isnadinsa, saboda a ciki jerin wadanda suka ruwaito shi akwai Sufyan bin Uyaina, wanda shi Sufyan sananne ne datadlisi a hadisai (wato boye aibobin da ke tattare da hadisi ko sanadinsa). Wannan shi ne abin da Zahabi ya tabbatar a cikin littafinsa Mizanul-l'itidal (2/170), har ma ya kara da cewa shi Sufyan bin Uyaina "ya kware da irin wannan aiki na tadlisi, kuma ba ya yin haka sai ta hanyar jingina wa mutanen da aka yarda da su." Dacewan malaman hadisi ne kuwa cewa tadlisi na daga mafi girman abubuwan dake raunana hadisi; don haka irin hadisin dake da wannan illa ba zai taba goge hukuncin AlKur'ani ba.

2. Yayi karo da abin da ya shahara daga Imam Ali [AS] na nacewarsa a kan halaccin auren mutu'a; ta yadda har maganarsa mai cewa: "Ba don cewa Umar ya hana auren mutu'a ba da babu wanda zai yi zina sai tababbe" ya zama ruwan-dare a tasakanin masu nazari a kan lamarin mutu'a. Don kore wa irin su R/Lemo shakka nake cewa a duba wannan zance na Imam Ali [AS] a tafsirin Tabari (5/13); da Tafsirul Kabir na Fakhruddin al-Razi (10/50); da tafsirin Durrul Manthur na Suyuti (2/140); da tafsirin Kurtubi (5/130) da wasu littafan hadisi irin su Nailul-Autar na Shaukani (3/250-251) da Subulul-Salam (sharhin Bulugul-Maram) na San'ani (3/967).

b) Sai ruwayar da ta zo ta hanyar Sabra bin Ma'abad al-Juhaniy: Shi ne hadisin Abdul-Malik bin Rabi' bin Sabra da ke cewa: "Manzon Allah [SAWA) ya umarce mu da yin mutu'a a shekarar da aka bude Makka yayin da muka shiga birnin Makka, amma ba mu fice daga cikinta ba har sai da ya hana mu yin auren na mutu'a." Wannan hadisi ya maiamaita da lafuzza makusanta ta yadda har ya wuce wanda ya gabace shi. Sai dai shi ma kamar wanda ya gabace shi ne, ba shi da kwarin da zai iya goge ayar AlKur'ani saboda dalilai masu zuwa:

1. Duk da yawan hanyoyinsa sai dai duk sun kare ne da Sabra daga babansa. Wannan ya sa hadisin ya zama cikin hadisan al-Aahad (wato hadisin da ya fito ta hanyar mutum daya) wanda malamai suka dace a kan cewa ba ya goge aya. Kara da cewa a daya daga cikin ruwayoyin na Sabra an ce huduba Manzo [SAWA] ya yi ga jama'a a tsakanin Ka'aba da Makamu Ibrahim; amma duk da haka babu wanda ya ruwaito wannan huduba sai Sabra shi kadai!

2. Sabra ya ruwaito shi ne daga babansa Rabi'u, wanda masana masu ruwayar hadisi suka kusan dacewa a kan cewa majhuli ne (wato ba a ma san shi ba). Wannan ma aibi ne dake raunana hadisi.

3. Ruwayoyin Sabra din suna karo da juna wajen fayyace lokacin da haramtawan ya faru; wasu daga cikin su sun ce ranar bude Makka, wasu suka ce a hajjin ban-kwana. Kara da cewa ya yi karo da hadisin da a kan dangana wa Ali, wanda zance a kansa ya gabata; saboda a can an dangana haramtawan ne da lokacin yakin Khaibara. Wannan duk da cewa wasu masu sharhin hadisan, irin su Ibin Hajar mai sharhin Bukhari, sun yi kokarin sama wa wannan mummanan karyata juna dake cikin hadisan dake haramta mutu'a mafita na cewa ta yiwu an maimaita hanin ne, sai dai wannan zato ne da bai dogara da wani dalili ba, taimakon da zai iya yi shi ne ya samar mana da shakka a kan haka; wanda ya fi wannan rauni shi ne fadar maimaita halattawan da haramtawan fiye da sau daya da wasu malamai (irin su Imamu Shafi'i a littafinsa Kitabul-Ummu). Da wannnan, ta yaya kuwa za a dogara goge tabbataccen hukuncin AlKur'ani da abin da ake shakka a kan tabbatarsa?

c) Sai Ruwayar Salma bin Akwa'u: Shi ne hadisin Musulim (a Littafin Aure, babin mutu'a), wanda a cikin isnadinsa akwai Yunus bin Muhammad da kuma Abdul-Wahid bin Ziyad, wanda ya ce: "Manzon Allah [SAWA] ya yi mana rahusa da yin auren mutu'a a shekarar bude Makka na kwana uku, sannan sai ya hana yin auren." Shi ma wannan hadisi kamar sauran 'yan'wansa ne, ba ya iya zama hujjar haramta mutu'a saboda raunin hanyar da ya fito (isnadinsa); domin daga maruwaitansa akwai Yunus bin Muhammad, wanda manyan masana masu ruwaya daga Ahlussuna guda uku suka raunana shi, wadannan kuwa su ne Ibn Mu'in da Nasa'i da Ahmad bin Hanbali (kamar yadda Zahabi ya bayyana a cikin Mizanul- I'itidal 4/485). Har ila yau a cikin maruwaitan nasa akwai Abdul-Wahid bin Ziyad, wanda shi ma bai sami yabo a wajen malaman fannin ba, saboda Zahabi ya ruwaito zantukan wadannan malamai suna zargin Abdul-Wahid da cewa ya shahara wajen kago insnadi na karya a ruwaya (duba Mizanul- l'itidal 2/ 672 wajen ambatonsa); haka Abu Dawud ya yi irin wannan magana a kansa; Yahya bin Mu'in ya kara da cewa "ruwayar Abdul-Wahid ba a bakin komai take ba" (duba duk wadannan bayanan a wancan littafi na Zahabi).

A kan wannan ka kiyasta kowane irin hadisi ka gani yana haramta mutu'a koda a littafan Shi'a ne kuwa. Ruwayar da R/Lemo ya yi ishara da ita a al-Istibsar da Tahzeebul-Ahakam na Sheikh al-Tusi (daga malaman Shi'a na karnin hijra na hudu), ko dai bai karanta su da kansa ba (da haka ya aikata abin da ya zargi Naziru Fagge da Safiya Gusau da aikatawa kenan) ko kuma ya zama shi ma ya kawar da kansa daga cewa wannan hadisi yana tsakiyar sama da hadisai ashirin a babobi daban daban na mutu'a kuma ya saba duk sauran (da haka zargin da ya yi ga wadancan 'yan'uwa biyu na kawar da kai daga hadisan dake haramta mutu'a a littafan Sunni ya fi cancantarsa); don kuwa: (a) a cikin wadannan littafai biyu kawai hadisin ya fito; (b) Kuma duk littafan biyu mutum daya ya wallafa su; (c) Sannan mawallafin ya tabbatar da rauninta bayan ya bayyana ta a cikin Tahzeebul-Ahakam, haka ya yi bayanin ma'anar wannan hanin a cikin al-Istibsar. Don haka babu abin da ke taimaka wa haramta mutu'a a duk littafan Shi'a.



back 1 2 3 4 5 6 next