Auren Mutu'a



Fadar Halaccin Mutu'a

Wadanda suke ganin hallacin auren mutu'a sun dogara ne da:

1. Ayar AlKur'ani (Nisa'i: 24) wadda duk Musulmi suka dace a kan cewa ita ta hallata mutu'a, amma suka saba a kan goge ta; kenan halattawan tabbatacce ne, haramtawan ne ake da shakka a kansa; babu inda shakka ke iya goge yakini.

2. Ga kuma tarin hadisai a kan halaccin auren, wadanda aka ambace su a tattaunawar da Naziru Fagge da Safiya Gusau suka gabatar kuma hatta irin su Ja'afar da R/Lemo ba su yi jayayya da su ko karyata su ba.

3. Cewa hadisan da ake dogara da su a kan haramcin mutu'a ba su inganta ba ta fuskar isnadi da ma'ana (don sun saba wa AlKur'ani), don haka ba su da karfin da za su iya goge hukuncin da ya tabbata a AlKur'ani.

4. Malaman Ahlul-baiti (wadanda 'yan Shi'a ke dauka a matsayin magadan ilimin kakansu) duk sun dace a kan halaccin mutu'a. Halattawarsu gare shi ne ma ya wanzar da tattauna wa a kansa a tsawon tarihin bincike da nazari. Da ma kuwa Annanbi [SAWA] ya fadi cewa ya bar mana su (Ahlul-baiti) tare da AlKur'ani, kuma ba za su taba rabuwa ba har su same shi a bakin tafkin Alkausara (Sahih Muslim 4/1873 hadisi na 2408).

5. Cewa akwai Sahabban da suka tafi a kan rashin shafe hukuncin mutu'a har suka bar duniya.

6. Kara da cewa kowane irin dalili ya sa Shari'a ta halatta mutu'a a jiya, to wannan dalili na nan a yau. Kuma bukatar mutu'a a yanzu (da hayoyin fitinuwa suka wayaita) bai kasa bukatarsa a farkon Musulunci ba idan ma bai wuce ba.

7. Cikar Musulunci da Musulmi suka yi imani da shi kuma wanda AlKur'ani ya tabbatar da shi (al-Ma'ida: 3) yana nufin cikakkun tanaje tanajen da Musulunci ya samar ne, wadanda za su magance wa Musulmi duk matsalolinsu na rayuwa. Idan aka ce Musulunci ne ya share mutu'a to an tuhume shi da samar da gibi ga mabiyansa, wanda bai musanya shi da wani abu mai tasiri ba. Saboda azumi yana rage kaifin sha'awa ne ba biyan bukatar jima'i ba; saboda mabukaci ko ya yi azumi yana da bukata idan ya yi bude-baki; kuma azumi ba ko da yaushe ake yinsa ba; sannan akwai masu uzurin da aka sauke musu azumin farilla ma balle na rage sha'awa. Halin matsi da matsan da ba su da ikon aure na dindindin kan shiga a lokacin fizgar balaga ba shi da magani sai mutu'a, in ba haka ba kuwa sai zina ko dabarun fitar da maniyyi da hannu (wanda ke haifar da cutar saurin gama jima'i ga da namiji da barazanar kau da sha'awar mace gare shi gaba daya) barnar wadannan lamurra ga daidaiku da al'umma kuwa bayyane yake ga kowa. Wannan ya kore soki-burutsun Ja'afar na kore mutu'a da rashin kawo wa matasa kakkarfar mafita.

Mutu'a A Furu'a

A nan ne nake son yin gyra a kan sigar da wannan tattaunawa take tafiya. Wani abu da masu tattaunawar suka rafkana daga gare shi shi ne cewa kallon mas'aloli irin wannan ya kamata ya fi bayar da karfi ne ta mahangar furu'a. Saboda daukar matsayin halattawa ko haramta abu irin mutu'a yana bukatar wasu ilmummuka da suka wuce harshen larabci da karanta hadisai da tafsiri. Akwai kusan fannonin ilimi har guda tara (wasu sun kai su har goma sha daya) da ya kamata mutum ya kware (ba kawai ya san wani abu a kansu ba) kafin ya yi fatawa da halal ko haram a furu'a.

Masifar da aka jarabci al'ummar Musulmi a 'yan shekarun nan shi ne na wasu 'yan Ustazai da suka fito daga wasu jami'o'in wasu kasashen Larabawa, bisa dogaro da kalkala da kadifiri na magana da harshen larabci sai suka shiga dora mutane a kan abubuwan da suka saba wa mazahabobinsu na furu'a. Wannan kuskure ne babba. Dole ne mutum ya koma ga daya daga wadanda aka dace a kan ikonsu na iya shiga cikin wadancan ruwayoyi masu karo da juna da samar da mafita, don aiki da abin da suka yi fatawa a kai. Dole Ahlussunna su koma ga malamansu (bai halatta su dauki fatawar wasunsu don jin dadi kawai ba), haka ma dan Shi'a wajibi ne ya dogara da fatawar marja'i a kan komai har da mutu'a. Wannan shi ne abin da duk bangarorin biyu suka dace a kai.



back 1 2 3 4 5 6 next