Auren Mutu'a



Kashi Na Biyu: Su ne ruwayoyin da suke dangana hana auren mutu'a da Khalifa na biyu Umar bin Khattab [RA]. Da alamun ambaton wannan ne ya fusata irin su R/Lemo har ya nemi karyata wannan dangane da tawilinsa. Sai dai duk wanda ya bibiyi wannan mas'ala da abubuwan da malaman Musulunci suka tattauna a kanta zai zama ba shi da hanyar karyata wannan dangane ga Khalifa [RA]. Misali, daga hadisan da Muslim ya fitar a wannan babin akwai hadisin Ibn Juraih daga Ibn Zubair, ya ce: Jabir bin Abdullah (al-Ansari) ya ce: "Mun kasance muna yin auren mutu'a da (sadakin) cikan tafin hannu na dabino da (nikakken) gari na 'yan kwanaki a lokacin Manzon Allah [SAWA] da lokacin Abubakr [RA], har zuwa lokacin da Umar [RA] ya hana a kan lamarin Amr bin Haris.

A wata ruwayar irin wannan da Muslim ya fitar, wadda Ahmad bin Hambali ma ya fitar da ita a cikin hadisan da ya kawo kan mutu'a, an nuna lokacin da Umar [RA] ya dauki wannan mataki da cewa "a karshen khalifancinsa ne" (duba duk wadannan a Sahih Muslim 4/131 a Littafin Aure, babin Mutu'a); haka wannan ruwaya ta zo a cikin Sunan na Baihaki (wajen ambaton hadisan mutu'a a Littafin Aure) da Tafsirin Kurtubi (wajen fassarar Ayar mutu'a) da wasunsu da yawa.

Gaskiya ne cewa wasu malamai sun ga ba makawa su koma da haramtawar zuwa ga lokacin Manzo [SAWA], da yin tawilin zantukan Khalifa Umar [RA] mai cewa "ina yin hani a kansu" da cewa yana nufin bayanin hanin da Shari'a ta yi ne, ba shi da kansa ba. Haka wadancan sun bayyana fadinsa da ya gabaci wancan din, wanda ya ke cewa: "Sun kasance" da cewa yana nufin a wani lokaci da ya gabata kafin a hana; da cewa Umar [RA] ya fadi haka ne a bisa mumbarin Manzo [SAWA] kuma a gaban Sahabbai, da dai masu sauraronsa ba su da labarin hani a kanta da sun yi korafi a kan haka. Sai dai duk wadannan tawile-tawile zasu rasa kowace irin kima idan aka yi la'akari da cewa:

1. Shi dai Khalifa da kansa bai fadi hanin Shari'a kafin zancensa ba; ya dai danagana wa kansa ne hanin; da kuwa akwai wani abu a Shari'a da ya haramta mutu'a da ba za a iya fahimtar abin da zai hana Umar [RA] ambatonsa a lokacin haninsa ba. Rashin dangana hanin ga Shari'a ya nuna haninsa ne kamar yadda ya bayyana haka a fili.

2. Ruwayoyin da ake dangana haramta mutu'a ga AlKur'ani da fadar Manzo [SAWA] duk mun tabbatar da ranuninsu a ka'idar ruwayar hadisi ta bangaren dukkan Musulmi.

3. A wani zancen na Umar [RA] da ya zo a cikin ruwayar da Baihaki ya fitar da ita a cikin Sunan dinsa (7/206), an hakaito Khalifa yana fusata bayan Khaulatu bint Hakim ta tsegunta masa auren mutu'a da Rabi'u bin Umayya ya yi da wata mace, a kan haka ne Khalifa ya fadi cewa: "Wallahi da na gabaci wannan mutu'an da na jefe shi a kansa." Wannan na nuna kafin khalifancin Umar [RA] babu hani a kan mutu'a.

4. Barazanar ukuba da Khalifa ya yi ga duk wanda ya kama da auren mutu'a ya nuna yaduwarsa a tsakanin Sahabbai (sabanin yadda Ja'afar da R/Lemo suke tsammani); abin da ke nuna Sahabbai ba su da labarin haramcin mutu'a kafin Khalifa ya hana; kuma barazana daga mai mulki ba a wasa da ita, shi yasa wasu Sahabbai suka kame daga mutu'a.

5. Cewa Sahabbai irin su Ibin Abbas [RA] da Jabir bin Abdullah al-Ansari da wasunsu sun yi karfin halin hamayya da matsayin Khalifa, inda suka ci gaba da fatawa a kan wanzuwar halaccin mutu'a. Abubuwan da wasu ke kokarin fada na cewa Ibin Abbas ya dawo daga halatta shi daga baya; da cewa Jabir ba shi da labarin haramcin ne ya sa ya nace a kan halatta shi, duk tawile tawile ne da ba su jingina da wani dalili ba; don haka ne ma malaman furu'a suka yi sakwa-sakwa da haramta mutu'a (ba su tsananta a kansa ba).

6. Zancen da Imam Ali [AS] ya yi ta nanatawa na cewa ba don hanin Khalifa ba da babu mai yin zina sai tababbe. Ka kuwa riga ka ji cewa dangana ruwayar haramta mutu'a gare shi rarrauna ne da ya fito daga wadanda aka zarga da tadlis da majhuli.

Wadannan kawai sun isa nuna cewa hanin na Khalifa ne, wanda shi ke da akalar mulki a hannunsa. Illa dai akwai uzurori da wasu ke ba Khalifa a kan haka, daga ciki akwai cewa ya yi wannan hani ne saboda wata maslaha da ta shafi wannan yanayin, don haka haninsa ba na dindindin ba ne. Wannan ya sa wasu daga malaman Ahlussunna (duk da su ne 'yan tsiraru) suka saura a kan halatta mutu'a.



back 1 2 3 4 5 6 next