Nuna Kauna Ga MutaneKamar yadda aka ruwaito da ingantaccen isnadi daga wajen Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Lalle cikan gaisuwa wajen mazaunin gida ita ce musafaha, sannan cikan gaisuwa ga matafiyi ita ce runguma[26]â€. Ba WaMutum Labarin Kaunar da Kake Masa
Na uku: labarin da mumini zai bai wa dan’uwansa mumini kan irin kaunar da yake masa, a wasu lokuta bayyanar da hakan ya kan kasance ne ta hanyar aiki, kamar musafaha, runguma da sumbanta kamar yadda ya gabata, a wasu lokutan kuma ya kan kasance ne ta harshen baki (magana) da ba shi labarin hakan. An ruwaito daga Abi Abdillah (a.s) da take nuni da hakan, inda yake cewa: “Idan kana son mutum ka sanar da shi hakan, don hakan ya kan tabbatar da soyayya a tsakaninkuâ€, a cikin wata ruwayar kuma ta daban “saboda hakan na dawwamar da soyayya da shakuwaâ€, a cikin na uku kuma cewa ya ke yi “Idan ka so wani daga cikin ‘yan’uwanka, to ka sanar da shi hakan, saboda (Annabi) Ibrahim (a.s) cewa ya yi: “Ya Ubangijina! Ka nuna mini yadda Kake rayar da matattu. Ya ce: shin, kuma ba ka yi imani ba ne? Ya ce: Na’am, kuma amma domin zuciyata, ta natsu[27]â€. |
back | 1 2 3 4 5 6 7 | next |