Nuna Kauna Ga Mutane



Abu Abdillah (a.s) yana cewa: “Allah (a.s) ya kasance Allah ce: ka da ku yi fushi sannan ka da ku sanya fushi, ku yada sallama tsakaninku, da kuma dadada Allah, ku yi salla da dare alhali mutane suna barci, za ku shiga Allah, daga nan sai ya karanta musu fadin Allah Madaukaki:M

﴿ السَّلَامُالْمُؤْمِنُ الْمُهَيْمِنُ﴾ [19]”.

Tafarki Na Biyu: Musafaha, Runguma, Sumbanta da Fada Wa Mutum Kaunar da Kake Masa

Ana kirga hanyar mu’amala tsakanin mutane yayin haduwa a matsayin tafarki na biyu, da ta hanyarsa za a iya tabbatar da kyakkyawar dabi’a da kyautatawa da kauna tsakani. A nan za mu shari’a ta jaddada wasu al’amurra da kwadaitarwa kansu don haduwa ta kasance hanyar tabbatar da soyayya da kyautatawa tsakanin al’umma, da bayyana hakan a matsayin kyakkyawar dabi’a.

Musafaha

Na farko: musafaha da mumini a lokacin da aka hadu da shi, wanda hakan na a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke nuni da kauna da yarda. An ruwaito Abi Ja’afar (a.s) cikin wani hadisi abin dogara yana cewa: “Lalle idan muminai biyu suka hadu suka yi musafaha da junansu, Allah Zai tarbe su da fuskarSa, sannan kuma zunubansu za su zube kamar yadda ganye ke fadowa daga bishiya[20]”.

Abu Abdullah al-Sadik (a.s) yana cewa: “Ku yi musafaha saboda tana tafiyar da kiyayya[21]”.

Akwai wasu ladubba da ka’idoji na musafahar da suka zo cikin nassosi, da ke nuni da muhimmancinta da kuma irin gudummawar da take bayarwa (wajen kyautata alaka ta zamantakewa) da kuma sanya ta a matsayin alama daga cikin alamu na Musulunci[22].

Rungumada Sumbanta

Na biyu: rungumar mumini da sumbantarsa a lokacin haduwa da shi don tabbatar da so da kauna, da kuma nuni da kyakkyawar dabi’a; an ruwaito wani hadisi daga Abi Ja’afar al-Bakir  da Abi Abdillah al-Sadik (a.s) suna cewa: “Duk wani muminin da ya fita don ziyartar dan’uwansa alhali yana sane da hakkinsa, Allah Zai rubuta masa ladan kowani taku da ya yi, ya kuma shafe masa zunubansa, ya kuma daukaka darajarsa, idan kuma ya kwankwasa kofa, za a bude masa kofofin sama, idan suka hadu suka yi musafaha da rungumar juna, Allah Zai tarbe su da fuskarSa, sannan Ya sanya mala’iku su yi alfahari da su ya ce: Ku dubi bayiNa sun yi ziyara da soyayya saboda Ni, don haka ya zama hakki a kaiNa da kada in azabtar da su da wuta bayan hakan…[23]”.

Haka nan an ruwaito Abi Abdillah (a.s) cikin wani ingantaccen hadisi yana cewa: “Hakika idan muminai suka rungumi junansu rahamar (Ubangiji) za ta rufe su, idan suka lizimci junansu alhali ba sa nufin komai face Allah, ba sa nufin wani abu na daga duniya za a ce musu: an gafarta muku su sake, idan suka fuskanci wata mas’ala mala’iku za su gaya wa junansu cewa: ku kauce daga gare su, saboda suna da wani sirri don Allah Ya rufe musu shi….[24]”.

An ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w.a) cikin kissar ganawarsa da dan baffansa Ja’afar bn Abi Talib (a.s) bayan Allah Ya ba shi nasara a Khaibar ta hannun dan’uwansa Aliyu bn Abi Talib (a.s) “Lokacin da Ja’afar bn Abi Talib ya dawo daga Habasha, Manzon Allah (s.a.w.a) ya mike ya tarbe shi da taku goma sha biyu, ya rungume shi ya kuma sumbanci tsakankanin idanuwansa, sai ya fashe da kuka ya ce: “Ban san da wani abu ne zan yi farin ciki ba, shin da dawowarka ne Ya Ja’afar ko kuma da nasarar da Allah Ya ba mu ne a Khaibar ta hannun dan’uwanka? Ya yi kuka don farin cikin ganinsa[25]”.



back 1 2 3 4 5 6 7 next