Nuna Kauna Ga MutaneHaduwa tana a matsayin tafarkin farko cikin alaka, saboda haka ne tsari da yanayin haduwar suka kasance matakin farko na kauna da soyayya. Musulunci ya kwadaitar da abubuwa daban-daban wajen tabbatar da hakan, da wadannan abubuwa masu zuwa suka kasance a kan gaba: Farawada Sallama
Na Farko shi ne farawa da sallama yayin haduwa da juna, an ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani hadisi abin dogaro yana cewa: “Wanda ya fara sallama shi yafi cancanta a wajen Allah da ManzonSa[12]â€. Kamar yadda aka ruwaito wani hadisi abin dogaro daga Imam Ali bn Husain (a.s) yana cewa: “Daga cikin kyawawan dabi’un mumini (Allah) fara yin sallama ga muminai[13]â€. Kamar yadda kuma aka ruwaito Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Farawa da sallama kafin magana, duk wanda ya fara magana kafin sallama, kada ku amsa masa[14]â€. Hakika Musulunci ya ba wa sallama muhimmanci na musamman, ya kuma sanya shi a matsayin taken musulmi, ya sanya masa ladubba da dokoki masu yawa don ta daukin matsayinta tsakanin musulmi. Mawallafin littafin Wasa’il al-Shi’a ya kebance babuka sama da ashirin don karin bayani kan wadannan ladubba da dokoki, yana da kyau a duba su[15]. A baya mun yi ishara da wasu karin bayanai, watakila a nan gaba mu samu damar sake ishara da wasu daga cikin yayin da za mu yi magana kan tsarin alamu da wajajen ibadar Allah. Haduwada Murmushi da Sakin Fuska
Na Biyu: haduwar musulmi cikin murmushi da sakin fuska, an ruwaito cikin hadisin al-Naufali daga al-Maskuni daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) Allah: Abubuwa uku suna nuni da kaunar mutum ga dan’uwansa musulmi: zai tarbe shi da sakin fuska da murmushi a lokacin Allah hadu da shi, zai buda masa wajen zama idan ya zauna kusa da shi, sannan kuma zai kira shi da mafi kyaun sunan da yafi so[16]â€. Zancen mustahabbancin murmushi ga mumini ma zai iya shigowa cikin wannan maudhu’i. An ruwaito Aba Ja’afar (a.s) yana cewa: “Murmushin mumini ga dan’uwansa abu mai kyau, kawar da abin cutarwa daga gare shi abu ne mai kyau; ba a bauta wa Allah da abin da ya fi shigar da farin ciki zuciyar mumini ba[17]â€. DadaddiyarMagana
Na uku: dadaddiyar magana yayin haduwa, kamar yadda aka jaddada batun fara sallama da dadaddiyar magana cikin ruwayoyi. An ruwaito Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Hakika Allah Madaukakin Sarki Yana son fara gaisuwa[18]â€.
|