Nuna Kauna Ga Mutane



Tafarki da Matakan Kauna da Kyautatawa

Idan muka ketare kulawa ta gaba daya da Musulunci ya yi wa batun kyawawan dabi’u, kauna da kyautatawa (ga sauran mutane), bari mu dawo don yin nuni da wasu tafarki da matakai na gaba daya da shari’ar Musulunci ya sanya don aiwatar da kyawawan dabi’u da kyautata tsakanin al’umma a aikace, hakan baya ga abubuwan da za mu yi ishara da su nan gaba wato kyautata wa mahaifi, don haka yana a matsayin mafi girman misali na kyawawan dabi’u, kyautatawa da kauna.

Ziyarada Saduwa da Juna

Bayani kan muhimmancin ziyarar juna wajen karfafa alaka ta zamantakewa a bangaren abubuwan da ke karfafa ginin al’umma, wanda ita ce kauna da soyayya. Saboda kwadaitarwar da aka yi kan ziyarar juna saboda tana tabbatar da batun haduwa tsakanin muminai ne, da kuma samar da dama ga kyawawan dabi’u da kyautatawa, kamar yadda aka ruwaito hakan daga Manzon Allah (s.a.w.a) cikin wasiyyar da yayi wa Ali (a.s) da ke nuni da muhimmanci ziyarar juna: “Ka yi tafiya mil hudu, ka ziyarci dan’uwanka saboda Allah[6]”.

Kamar yadda muka kawo a baya daga Shu’aib al-Ukrikufi cikin hadisin da ya ruwaito daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: Ku yawaita ziyara da haduwa da junanku[7]”.

Daga Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Haduwa tsakanin ‘yan’uwa yayin zaman gida (ba cikin tafiya ba) ita ce ziyarar juna[8]”.

Haka nan an ruwaito daga gare shi (a.s) cewa daga cikin hakkokin musulmi a kan dan’uwansa musulmi shi ne “idan ka ganshi, ka ziyarce shi[9]”.

Kamar yadda aka ruwaito da wajensa (a.s) yana cewa: “Kada ka gaji (kosa) da ziyartar ‘yan’uwanka; saboda idan mumini ya hadu da dan’uwansa ya ce masa: barka (da war haka ko barka da zuwa), za a rubuta masa barka har zuwa Ranar Kiyama, idan kuwa suka yi musafaha (gaisuwa ta hannu da hannu), Allah Zai aiko da rahama dari tsakankanin manyan ‘yan yatsunsu, casa’in da tara daga cikinsu don na karin dankon zumunci da soyayya tsakaninsu, sannan Allah Zai tarbe su da fuskarSa, wanda ya fi dan’uwansa kauna gare shi zai fi samun wannan tarba, idan kuwa suka rungumi juna rahamar (Allah) za ta rufe su[10]”.

Ahlulbaiti (a.s) sun sanya wata manufa ta gaba daya cikin wannan ziyarce-ziyarce, haduwa da kyautatawa tsakanin mutane, ita ce kuwa samar da matakin koli na kauna, soyayya da alaka ta ruhi tsakanin mutane, ta yadda Imam Ali (a.s) yana bayyana hakan cikin Nahjul Balaga da cewa: “Ku zauna da mutane irin zaman da idan kun mutu za su yi kukan (rabuwa da ku), idan kuwa ka rayu za su zo gare ku (za su kaunace ku)[11]”.

Yana da kyau a san cewa wannan kyautatawa ba wai kawai ta bayyane b ace ballantana har a yi tunanin saboda samun wani amfani na mutum shi kansa ne yake yi ko kuma don munafunci ba, face dai aiki ne da ke da wata manufa ta hakika ita ce kuwa so da kauna.

Bisa la’akari da cewa wannan ziyara da kuma haduwa suna da matsayi na musamman cikin alaka ta zamantakewa, da kuma wata gudummawa ta musamman cikin kyawawan dabi’u da kyautatawa, don haka ne za mu ga shari’a ta sanya wasu ka’idoji da dokoki masu kyau da za su samar da mafi kyawun sakamako da natija ta wannan ziyara, hakan kuwa cikin wadannan matakai masu zuwa ne:

Tafarkin Farko: Haduwa Cikin Murmushi da kuma Sallama



back 1 2 3 4 5 6 7 next