Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3



Bayan wannan ma idan mun dauka cewa bayan addu’ar da Manzo ya koyar da wannan makaho shi ma ya yi wa makahon addu’a, a nan ba zai cutar da kafa hujjar da muka yi ba da wannan hadisi, domin kuwa ba muna magana ne ba a kan addu’ar da Manzo ya yi masa. Domin kuwa muna kafa hujja ne a kan addu’ar da Manzo ya koyar da makaho ta yadda ya koyar da shi yadda zai yi kamun kafa da shi kansa Manzo sakamakon matsayi da daukaka da yake da shi a wajen Allah.

Idan da zaka bai wa wani masanin harshe wannan hadisi wanda ba shi da wata masaniya a kan haka, babu abin da zai fahimta bayan kamun kafa da Manzo (s.a.w) a wajen Allah madaukaki.

Ibn Taimiyya da mabiyansa lokacin da suka fuskanci wannan hadisi sun yi kokari su kawo matsala dangane da ma’anar wannan hadisi dangane da jumlolin da suke nuni a kan kamun kafa da Manzo a fili, sai su ce yana nufin addu’a ne, suna cewa:

Jumlar da take cewa: “Ina fuskantarka da manzonka” sai su ce wai ina fuskantarka da addu’ar manzonka.

A wannan akwai wani abin da ba a fada ba wannan kuwa shi ne sun yi hukunci ne sakamakon akidar da suke da ita tun da farko na haramcin kamun kafa da waliyyan Allah, amma wannan tawili nasu sam bai dace ba da jumlolin da muka ambata dangane da hakan.

Idan kuwa gaskiya ne makaho ya yi kamun kafa ne da addu’ar Manzo, to me ya sa Manzo ya ce masa ka ce: “Muhammad annabin rahama” sannan ya ce masa ka ce: “Ya Muhammad lallai ina fuskantarka”

Bayan wannan idan muka dauka ma’anar wannan yana nufin addu’a ne, to wannan zai bata tsarin jumlar.

Alusi Bagdadi (ya rasu 1270) wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka yada wahabiyanci a nan yana mika wuya zuwa ga gaskiya, inda ya tafi a kan cewa kamun kafa da waliyyan Allah Manzo ne ko waninsa ba shi da wani laifi, da sharadin cewa mu dauka wannan mutumin yana da matsayi ne a wajen Allah[12].

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next