Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3Abin da ake nufi da shirka kuwa a cikin wannan tambaya da tagabata shi ne shirka a cikin ibada, (hadallah da wani a cikin bauta) wato neman addu’a daga mamaci yana nufin yi masa bauta kenan. Wannan tunani na sama sam ba ya inganta, saboda: Na farko: Idan neman addu’a ga mamaci yana nufin yi masa bauta, to wannan ya nuna cewa neman addua’a daga mutumin da yake a raye shi ma yi masa bauta ne domin kuwa babu bambanci, domin kuwa neman addu’a ne tare da kaskantar da kai, don haka wadanda suke ganin neman addu’a daga wanda yake raye ba ya nufin bauta masa ba ne, don haka dole ne su amince da cewa yin hakan bayan rasuwa ma ba yana nufin bauta ba ne, ballantana ya zama shirka ko sabanin tauhidi. Na biyu: A cikin fasali na hudu na wannan littafi mun bayani a kan ma’anar ibada bisa dalilai na hankali, ta yadda muka nuna cewa ba duk neman wani abu ko addu’a ko makamancinsa ba ne ibada. Abin da ake nufi da ibada shi ne wani nau’i ne na girmamata musamman wacce take tare da wata akida ta musamman, wato mutum ya dauki wanda yake kaskantar da kansa a gare shi a matsayin Allah, wa’iyazu billah, ko kuma mutum ya dauka cewa wani abin halitta ne yake tafiyar da wasu daga cikin ayyukan Allah kamar yadda masu bautar gumaka suke dauka. Amma girmamawa da kaskantar da kai wanda ya koru daga wannan akida marar tushe, ta yadda mutum yana ganin wanda yake girmamawa a matsayin wani bawan Allah ne, kuma wanda yake da kusanci zuwa ga Allah, sakamakon haka ne yake kamun kafa da shi yana neman addu’arsa, sam ba a kiran wannan bauta, ballantana ya zama shirka da Allah. Tambaya ta biyu: Shin neman addu’a daga mamaci ba shi da wani amfani? Daya daga cikin abin da masu inkarin wannan al’amari suke kawowa shi ne, mutumin da ya mutu sam ba shi da ikon da zai iya biya wa mutum bukatarsa. Saboda haka neman wani abu daga wanda ya mutu sam wani abu ne marar amfani. Amsa: Tushen wannan tamabaya yana komawa ga yadda mutum yake ganin duniya, wato kamar cewa wannan duniyar da muke gani ita kawai ce duniya bayan wannan babu wani abu, wdan da suke kuma ganin cewa mutum da zarar ya mutu shi kenan babu sauran wata rayuwa, don haka wadanda suka gabata sama ba su da wata rayuwa, don haka neman wani abu daga gare su wani abu ne marar amfani. Amma tare da kula da ka’idojin da muka ambata a sama, amsar wannan tambaya a fili yake, haka ne mutum da ya mutu ba shi da rayuwa irinta duniya, amma yana da wata rayuwar ta lahira, sannan tare da izinin Ubangiji yana iya amsa na bukatocinmu. Tambaya ta uku: Shin tsakanimmu da wadanda suka rasu akwai wani shamaki wanda zai hana su jin maganarmu?
|