Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3Abin burgewa a nan shi ne almajirin Ibn Taimiyya wato Ibn Jauziyya, shi ma a cikin littafinsa (Arruh) ya fassara wannan aya da ake tambaya a kanta kamar yadda muka fassara. [8]Yarda da wannan tafsiri da Ibn jauziyya ya yi, yana nuna kaucewa daga ra’ayin malaminsa Ibn Taimiyya a kan wannan magana. 7-Kamun kafa Da Mutane Tsarkaka Da Mutane Masu Daraja Bahsin da ya gabata an yi magana ne dangane da kamun kafa da addu’ar mutane masu tsarki da daraja, wato wanda yake da wata bukata yana neman su yi masa addu’a domin Allah ya biya masa bukatarsa, wato addu’arsu zata sanya ya samu kusanci. Amma abin da muke magana a kansa a cikin wannan Bahasi shi ne yin kamun kafa da su kansu don samun kusanci zuwa ga Allah madaukaki. Wato mai neman biyan bukata ba tare da ya nemi addu’arsu ba domin ya samu biyan bukatarsa, sai ya yi kamun kafa da su domin kasantuwarsu suna da matsayi a wajen Allah, sakamakon haka sai ya nemi abin da yake bukata a wurin Allah madaukaki, ta hanyar wannan matsayi da daukaka da suke da su a wajen Allah, sai Allah ya biya masa bukatarsa. Wannan nau’in kamun kafa kuwa ana yin sa ta hanyoyi daban-daban kamar haka: Ya Allah don matsayin da suke da shi a wurinka! Ya Allah don kusancin da Masoyanka waliyyanka suke da shi a wurinka! Ya Allah albarkacin manzonka da iyalansa tsarkaka! A cikin dukkan wadannan jumloli shi kan shi mutum wanda yake da matsayi a wurin Allah da siffofinsa masu kyawu su ne zasu sanya a biya wa mutum bukatarsa, bayan shaharar wannan nau’i na kamun kafa, akwai ruwaya ingantacciya da ta zo a kan haka wacce ake kira da “dharirâ€harda kuwa wadanda suke da sabani a kan wannan al’amari sun tafi a kan ingancin wannan ruwaya. Domin kuwa mun kawo yadda aka kafa hujja da wannan hadisi zamu kawo wannan hadisi a nan kamar haka: Usman Bn Hanif yana cewa: Wani mutum makaho ya zo wajen Manzo (s.a.w) ya ce ya manzon Allah ka yi mini addua’a Allah ya ba ni waraka. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Idan kana so zan yi maka addu’a idan kuma zaka yi hakuri shi ne abin da ya fi. Sai wannan makaho ya ce ka kira Allah ka yi mini addu’a! A wannan lokaci sai Manzo ya ce: ka je ka yi alwala mai kyau, sannan ka yi salla raka biyu ga wata addu’a nan ka karanta.
|