Kamun kafa Da Annabawa Da Waliyan Allah 3Sannan a bahsimmu da ya gabata mun tabbatar da kasantuwar alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ta yadda suna jin duk abin da muke fada. Tare da kula da abin da muka ambata, ayar da muka ambata a baya ba ta kebanta da lokacin rayuwar Manzo ba, kuma riko da hakan wani abu ne marar dalili. Sannan zamu tambayi wadanda suke inkarin kamun kafa da Manzo da cewa: me ya sanya bai halatta a yi kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa ba? Shin don ya kasance ne duk wani girma da daukaka da kusanci ya samu ne a gare shi sakamakon yanayin jikinsa ne, ta yadda sakamakon rasuwarsa wannan matsayin da kusancinsa a wurin Allah zai kawo karshe?! Shin mutuwa shi ne karshen rayuwar mutum ta yadda Manzo bayan wafatinsa ba shi da sauran rayuwa?! Shin sakamakon wafatin Manzo shi kenan ba mu da sauran wata alaka da shi?! Amsar dukkan wannan tambayoyi kuwa ita ce; a ‘a, don haka dole ne mu amince da cewa kamun kafa da Manzo a dukkan lokuta guda biyu (rayuwa da rasuwarsa) babu bambanci. Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa, Sheikh Khalil Ahmad saharnafuri ya tattara fatawowin malaman AhlusSunna 75 dangane da halascin kamun kafa da Manzo. A cikin wannan littafi da muka ambata a sama, an yi Karin bayani da cewa: A nazarimmu da manyan malamammu shi ne, ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan hanyoyi wajen neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki, sannan yana daya daga cikin muhimman ayyuka masu lada kuma wata hanya ce domin samun matsayi da daraja madaukakiya. Wannan kuwa wani umarni ne wanda yake kusa na wajibi da farillai na shari’a, madamar isa zuwa ga hakan ba zai janyo tsanani ko asarar rayuwarka ba. Kamun kafa kuwa da annabawa da waliyyai da manyan bayin Allah, shahidai da siddikai, a cikin addu’a a lokacin rayuwarsu ne ko kuwa bayan rayuwarsu ya halatta. [2] Tambayoyi Da Amsoshi Dalilai a kan halascin kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa wani abu ne wanda ya bayyanar mana. Amma dangane da hakan akwai wasu tambayoyi wadanda dole ne mu bayar da amsarsu. Tambaya ta farko: Shin neman addu’a daga mamaci shirka ne? Wasu suna tunanin cewa neman addu’a daga wanda yake raye, wato yana iya yin addu’ar wani abu ne wanda ya halasta, amma yin haka ga mamaci shirka ne. Amma shin wannan tunani daidai ne?
|