Umar da Ra'ayin Shari'a 2Mutane su ka yi yaki mai tasnani, hamza da abudujanata su ka yi yaki mai tsanain a cikin jama'ar musulmi, kuma Allah ya saukar da nasararsa a kansu, kuma aka rusa mushrikai gaba daya, mata su ka gudu zuwa duwatsu, musulmi su ka shigga rundunarsu su na masu tara ganima, kuma yayin nan ne sai masu harbi su ka ga 'yan'uwansu masu yaki su na kwasar ganima, sai su ka zabi zuwa su dibi ganima a kan su wanzu a kan inda manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya dakatar da su, kuma ya kwadaitar da su da tsayawa a wurin. Yayin da Khalid dan Walid ya ga karancin masu harbin musulmi sai ya kai hari kan wadanda su ka rage ya kashe su baki daya, kuma ya kai hari da shi da wadanda su ke tare da shi kan shabban manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ta baya, kuma sai wadanda su ka gudu daga mushrikai sua samu kwarin gwiwa su ka dawo da yaki sabo kan musulmi har sai da su ka rusa muslmi bayan sun kashe mutane saba'in daga gwarazan musulmi, daga cikinsu akwaizakin Allah da manzonsa sayyidi hamza dan abdulmudallib, kuma manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi yaki mai tsanani, ya yi harbi da kibiya har sai da ta kare, kuma tsirkiyar kwarinsa ta tsinke, aka same shi da raunuka a kumatunsa, da wani a goshinsa, da karye hakoransa na kasa, da yage lebensa, kuma Ibn kami'a ya same shi da takobi a kansa. Kuma Ali ya yakin kare shi, a tare da shi akwai mutanen biyar na ansar (mutanen madina) da su ka yi shahada wurin kare shi (Allah ya yarda da su), kuma abudujanata ya kare manzon Allah da kansa da jukinsa, sai ya kasance kibiyoyi su na fadawa kansa shi kuma ya na rufe da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), mus'ab dan umair ya yi yaki har sai da ya yi shahada, Ibn kami'a allaisi shi ne ya kashe shi ya na tsammanin shi ne manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) don haka ne ma ya koma ya na cewa da su: Na kashe muhamamd, sai mutan su ka rika cewa: An kashe Muhammad, an kashe Muhammad, sai musulmi su ka fara yaki ba tare da wani sanin hakika ba, kuma farkon wanda ya gane manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) shi ne ka'abu dan malik yayin nan ya yi magana da sautin mai karfi ya ce: Ya ku jama'a musulmi ku yi albihsir ga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) nan rayayye ba a kashe shi ba, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi masa nuni da ya yi shiru[14]. A lokacin nan ne Ali da wadanda su ke tare da shi su ka tashi su ka fitar da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) zuwa ga wani kwararo, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya samu yin kariya da shi, su kuma su na kewaye da shi su na masu kariya gare shi. Ibn jarir, da Ibn asir da sauran masu littattafan tarihi littattafan tarihinsu su na cewa: Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya duba - a lokacin ya na cikin lokon - ya hango wasu mutane daga mushrikai sai ya ce da Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi): Kai musu hari, sai ya kai musu hari ya tarwatsa jama'arsu, ya kashe wasu daga cikinsu, sannan sai ya sake ganin wasu jama'ar ya ce da Ali: Isar mana da su ka kai musu hari: Sai ya kai musu hari ya tarwatsa su ya kashe wasu cikinsu, sai Jibril ya ce: Ya ma'aikin Allah wannan duk 'yan'uwantaka ce. Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Shi daga gare ni ya ke, ni man daga gare shi na ke, sai jibril ya ce: Ni daga gare ku na ke. Sai aka ji wani sauti ya na cewa: Babu takobi sai Zulfikar, kuma babu wani saurayi sai Ali. Sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya rika kai ruwa ga manon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) a cikin garkuwarsa ya na wanke jinin manzon Allah da shi amma jinin bai tsaya ba[15]. Amma Hindu da matan da su ke tare da ita sai ta hau kan shahidai ta na yi musu musula, sai ta rika yanke kunnuwa da hancina da hannaye da kafafuwa da azzakarinsu, da duk abin da ya ke rataye da su, kuma ta na ba wa Wahshi abin da ta ke ratayawa na wuya saboda ya kashe hamza, ta fasa cikin hamza ta fitar da hanta ta tattauna ba ta hadiye ba sai ta furzar. Sannan sai abusufyan ya zo ya cewa musulmi shin akwai Muhammad a cikin mutane? Sau uku, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) [16] ya ce: Kada ku ba shi amsa[17]. Sai abu sufyan ya ce: Ina hada ka da Allah ya Umar shin mun kashe Muhammad? Sai Umar ya ce: Ba haka ba ne, kuma wallahi ya na jin maganarka. A nan ne na ce: Wannan shi ne abin da na ke son kawowa, na yadda ya zabi fifita ra'ayin abusufyan a kan hanin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) na kada ya bayar da amsa kamar yadda ake iya gani.
|