Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Ya kasance idan ya sanya Ali jagora a wani yaki ko wani hari to sai ya hada amsa wata tutar ta wasu ma'abota rigo zuwa musulunci ya sanya su karkashinsa, amma idan ya sanya wani jagora ga wata jama'a, to ba ya sanya Ali karkashinsa. Kamar yadda ya yi a yakin Haibar yayin da ya sanya Abubakar jagora sai ya gudo, haka ma ya sake tura Umar shi ma ya gudo, a nan duka bai sanya Ali karkashinsu ba. Amma da ya aika Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) a karo na uku bayan yabon da ya yi masa na cewa Allah (Mai Girma da Buwaya da Daukaka) da manzo (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) su na son sa, shi ma ya na son Allah da manzonsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi), sai ya sanya Abubakar da Umar karkashin tutarsa. Godiya ta tabbata ga Allah kan wannan duka!.

Haka nan idan ya sanya runduna guda biyu, daya a karkashin jagorancin Ali daya kuma karkashin jagorancin wani, to yakan gaya musu cewa idan su ka hadu to jagorancin duka rundunar biyu ya na karkashin Ali shi kadaia, amma idan su ka rabu to kowa ya na kan jagorancin rundunarsa[12].

Kuma sau da yawa yakan aika waninsa sai ya dawo da rundunarsa bai samu budi ba, sai a aika Ali bayansa sai ya samu budi da nasara mai yawa, wannan kuwa don ya nuna fifikonsa da waninsa ba shi da shi, wanda da ya aika shi tun farko da wannan fifikon bai bayyana ba.

Kuma ya na iya aika waninsa kan wani muhimmin lamarin da mutane su ke ganin muhimmancinsa, sai Allah ya yi masa wahayi da cewa: Kada wani ya kai wannan sakon sai kai ko wani mutum daga gare ka ya na nufin Ali, kamar yadda ya kasance kan lamarin "Bara'a" daga Allah da manzonsa daga mushrikai, da jefar da alkawari ranar Hajji mafi girma[13].

 

Daga ciki, haninsa ga sahabbansa ga ba wa abusufyan amsa a yakin uhud

Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kasance ya sauka rana uhdu da shabbansa - su dari bakwai - a udwatul wadi, ya sanya bayansa a bayan dutse, mushrikai sun kasance kusan 3000 ne, akwai masu sulke 700 a cikinsu, da mahaya dawakai 200, da kuma mata 15. Amma a musulmi akwai mai sulki da mahaya dawakai 200 ne kawai.

Runduna biyu ta gaji da yaki, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya fuskancin madiina ya bayar uhud ba bayansa, ya sanya masu harbi su 50, da ya sanya abdullahi dan Jubai jagora kansu, ya gaya masa cewa: Ka kare mana dawakai da kibau, kada su zo mana ta bayanmu, ku tabbata wurinku, idan mun ci nasara ko an ci mu da yaki, ka sanci za a iya zo mana ne kawai ta wannan lokon wato lokon uhudu.

Sai Dalha dan usamn mai tutar mushrikai ya fito ya na cewa: Ya ku shaabban Muhammad ku ka na raya cewa Allah zai gaggauta mu zuwa wuta da takukbbanku, ya gaggauta ku zuwa aljannan da takubbanmu, shin akwai wani daga cikinku da zai gaggawta zuwa aljannna da takobina, ko ya gaggauta ni zuwa wuta da takobinsa?

Ibn Asir ya na fada a littafinsa na alkamil cewa: Sai Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya yi masa mubaraza sai ya doke da takobi sai ya cire kafarsa sai ya fado ya bayyanar da al'aurarsa, sai ya hada shi da Allah ya kyale shi, sai ya bar shi - yayin da yyya ga ya na zubar kwararar jini har sai ya mutu - sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi kabbara ya ce: Jagoran yaki ke nan, kuma musulmi su ka yi kabbara da kabbararsa, kuma ya ce da Ali: Me ya hana ka ka kai masa hari? Sai ya ce: Ya hada ni da Allah ne da kuma kusancin zumunci, sai na ji kunyar sa.

Ali ya dage ya tattaba bayan nan ya na mai kai hari kan masu tuta ya na gamawa da su daya bayan daya. Ibn Asir da waninsa ma sun ce: Musulmi sun kashe masu tuta daya bayan daya, har sai ya kasance a kasa babu wani daga kafirai da ya ke kusantar ta, sai Umra 'yan alkama alharisiyya ta dauki tutar, sai ta daga ta, sai kuraishawa su ka taro a gefenta ta, sai wani bawan Banu Abduddar mai su na Sawab ya dauki tutar, ya kasance daga mafi karfin jarumawansu, shi ma sai ya yi yaki a kan kare ta, ya kasance wanda ya kashe duk wani wanda ya dauki tutar kafirai shi ne Imam Ali dan abu Dalib (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi), kamar yadda Abu Rafi'I ya kawo a tarihi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next