Umar da Ra'ayin Shari'a 2



Daga ciki, ture wa Mugira dan Shu’uba haddi

Wannan kuwa saboda abin da Mugira dan Shu’uba ya yi ne (tare da cewa ya na muhsini) tare da Ummu jamil 'yar amru, wata mata daga Kais a labarin da ya ke ya na daga mafi shaharar labarin tarihi a larabawa, wannan kuwa ya kasance a shekara ta 17 bayan hijira, kuma babu wani littafin da ya kawo abubuwan da su ka faru a wannan shekarar da bai kawo shi ba, kuma dukkan shedu sun shaida kan hakan da su ka hada da Abubukarata, wanda ya na daga cikin manyan sahabbai, da su ke dauke da ruwayoyi daga annabi, da kuma Nafi'u dan haris wana shi ma sahabi ne, da kuma Shiblu dan ma'abad, wannan dukkan su sun bayar da sheda a fili karara na abin da su ka ga ya na shiga ciki kuma ya na fita kamar shigar mashiyi cikin tandu, bau wta kinaya, babu wani kumbiya - kumbiya. Amma da batu ya zo kan na hudu wato ziyad dan sumayya don ya bayar da sheda, sai halifa ya yi masa nuni da kwadaitar da shi da cewa kada ya kunyata Mugira, sannan sai ya tambaye shi abin da ya gani tukun, sai ya ce: Na ga wani zama, kuma na ji wani lumfashi mai karfi da ajiyar zuciya, na gan shi ya kifa kanta. Sai Umar ya ce: Shin ka gan shi ya na shigar da shi ya na fitar da shi kamar mashiyi cikin tandu? Sai ya ce: A'aha. Sai dai na gan shi ya daga kafarunta sama, kuma na ga golakensa su na yawo a tsakanin cinyoyinta, kuma na ga wani rikon motsi mai tsanani, kuma na ji wani sauti mai karfi. Sai Umar ya ce: Ka ga ya na shiga ya na fita kamar mashiyi cikin tandu? Sai ya ce: A'aha. Sai Umar ya ce: Allahu akbar ta shi ya kai Mugira ka ta fi wurinsu ka yi musu bulala. Sai ya tsayar musu da haddi.

Ku duba labarin wannan lamarin dalla - dalla da lafazin alkali Ahmad asshahir dan khalikan a littafinsa - wafayatul a'ayan - yayin da ya fadi wannan abin da lafazinsa ya ke kamar haka:

Amma batun Mugira dan Shu’uba da yin shaida kansa, hakika Umar dan kahddabi ya kasance ya sanya Mugira amiri kan basara, kuma ya kasance ya na fita daga gidan sarautarsa a rabin rana. Abu bukrata ya kasance ya na haduwa da shi sai ya ce: Ina kuma amir zai ta fi? Sai ya ce: Wata bukata ce. Sai ya ce; ai amir shi ne ake ziyara shi ba ya ziyara. Ya ce: Ya kasance ya na zuwa uwrin wata mata ce da ake ce wa da ita ummu jamil 'yan amru, mijinta shi ne hajjaj dan atik dan alharis dan wahab aljashami, sannan sai ya kawo nasabarta. Sannan abubukrata ya ruwaito cewa ya na cikin daki da shi da 'yan'wuansa, da nafi'u, da ziyad, da shibl dan ma'abad, 'ya'yan sumayya wadanda su 'yan'uwa ne ta wurin uwa, kuma ummu jamil da aka kawo bayaninta ta kasance a daya dakin da ya ke daura da dakin da su ke, sai iska ta daga kofar dakin ummu jamil, sai ta bude shi, sai mutane su ka duba sai ga Mugira da matar su na kan yanayin yin jima'I, sai abubukrata ya ce: Wannan ne bala'in da aka jarrabe ku da shi, ku duba, sai su ka duba har su ka tabbatar, sai abubukrata ya sauka ya zauna har sai da Mugira ya fito sai ya ce masa: Lamarinka ya kasance kamar yadda ka sani, don haka ka bar mu. (Ya ce): Sai Mugira ya ta fi don ya yi sallar azahar da mtuane, sai abubukrta ya wuce. Abubukrata ya ce: Wallahi ba za ka yi salla da mu ka yi abin da ka yi. Sai mutane su ka ce: Bar shi ya yi salla da mu, ai shi ne amir, ku rubuta wa Umar game da shi, sai su ka rubuta wa Umar sai ya umarce su da su gabata baki daya, Mugira da shedu dukansu, yayin da su ka zo wurin majalisin Umar, sai ya kira shedu da Mugira, sai abu bukrata ya gabata. Sai ya ce masa: Ka ga tsakanin cinyoyinta? Ya ce: Na'am. Wallahi kamar ina ganin tsagun tattarar fatar cinyarta, sai Mugira ya ce masa: Ka duba sosai kuwa? Sai abubukrata ya ce: Ba zan gushe ba sai na tabbatar da abin da Allah zai kunyata ka da shi. Sai Umar ya ce: A'aha wallahi har sai ka shaida da cewa ka gan shi ya na shiga kamar shigar mashiyi cikin tandu. Sai ya ce: Na'ama na shaida da hakan.

Sai ya ce: Ta fi Mugira domin rubu'inka ya ta fi. Sai ya kira nafi'u sai ya ce masa: A kan me za ka shaida? Sai ya ce: A kan irin abin da abubukrata ya sheda. Sai ya ce: A'aha, har sai ka sheida cewa ka ga ya na shiga ya na fita kamar shigar mashiyi ckin tandu. Sai ya ce: Na'ama har sai da ya kai karshen zurfinsa. Sai Umar ya ce da shi: Ta fi Mugira domin rabinka ya ta fi. Sannan sai ya kira na uku, ya ce masa a kan me za ka shaida? Sai ya ce: A kan irin shaidar abokaina. Sai Umar ya ce amsa: Ta fi Mugira kashi uku cikin hudu naka ya ta fi.

Sannan sai Umar ya rubuta ya aika wa ziyad da ya zo, ziyad ya kasance ba ya nan sai ya zo, yayin da ya gan shi sai ya zaunar da shi a masallaci, kuma manyan sahabbai muhajirun da ansar su ka taru gun sa a masallaci, yayin da Umar ya hango ziyad ya na tahowa sai ya ce masa: Ni ina ganin ka mutum ne da Allah ba zai kunyata wani mutum daga muhajirai ta harshensa ba.

Sannan sai Umar ya daga kansa zuwa gare shi ya ce: Meye gun ka ya kai mafedin talatalon daji! An ce Mugira ma ya tashi zuwa ga ziyad ya ce masa: Babu boyewa ga turare bayan angwanci. Mugira ya kara ce masa: Ya kai ziyad ka tuna Allah, kuma ka tuna tsayuwarka ranar alkiyama, ka sani Allah da manzonsa da sarkin muminai sun tsare jinina sai dai idan kai ne ka ketare zuwa ga abin da ba ka gani ba zuwa ga abin da ka gani, kada mummunan gani ya sanya kaa ketarewa zuwa ga abin da ba ka gani baa, kuma na rantse da Allah da ka kasance tsakanin cikina da cikinta to da ba za ka ga shigar zakarina cikinta ba. Ya ce: Sai hawaye su ka zuba daga ziyad, kuma fuskarsa ta yi ja, sannan ya ce: Ya kai sarkin muminai amma dai mafi gaskiyar abin da mutanen su ka kawo ni ban kai gare shi ba, ni dai na ga wani zama, kuma na ji nishi mai tsanani mai sauri, da wani gunji, sai na ga na kifa kan juna. Sai Umar ya ce da shi: Shin ka ga ya na shiga ya na fita kamar mashiyi cikin tandu? Sai ya ce: A'aha. An ce: Ziyad ya ce: Sai dai na gan shi ya daga kafarunta sama, kuma na ga golakensa su na yawo a tsakanin cinyoyinta, kuma na ga wani rikon motsi mai tsanani, kuma na ji wani sauti mai karfi. Sai Umar ya ce: Ka ga ya na shiga ya na fita kamar mashiyi cikin tandu? Sai ya ce: A'aha. Sai Umar ya ce: Allahu akbar ta shi ya kai Mugira ka ta fi wurinsu ka yi musu bulala. Sai ya samu abubukrata ya yi masa bulala tamanin, ya kuma yi wa sauran. Kuma maganar ziyad ta kayatar da Umar ya kore wa Mugira haddi. Sai abubukrata bayan an yi masa haddi ya ce: Na shaida na ga Mugira ya yi kaza da kaza. Sai Umar ya yi nufin sake yi masa haddi na biyu, sai Ali dan abudalib (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya ce masa: Idan ka doke shi, to ka jefi sahibinka, sai ya bar shi. Umar ya nemi abubukrata ya tuba, sai ya ki ya ce: Ka na neman in tuba ne saboda ka karbi shaidata nan gaba. Sai ya ce: Haka ne. sai abubukrata ya ce: Ni ba zan sahek yin sheda tsakanin mutum biyu ba matukar ina raye a duniya, yayin daak yi musu haddi sai Mugira ya ce: (Allahu akbar, Alhamdu lil - Lahi) girma ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kunyata ku. Sai Umar ya ce masa: Allah ya yi wadaran yanayin da su ka gan ka a kansa.

(Ya ce): Umar dan shaiba ya kawo a littafin "Akhbaru Basra": Cewa: Babar abubukrta ta yanka akuya ta sanya masa a bayansa saboda zafin bulala da ke bayansa, ana cewa wannan kwua saboda tsananin duka ne. ya ce: Abdurrahman dan abubukrata ya na cewa: Babanwa ya rantse da Allah ba zai sake yi wa ziyad magana ba matukar ya na raye, yayin da abubukrata ya rasu, sai ya yi wasiyya da kada wani ya yi masa salla sai abu barzatal salami, ya kasance shi ne wanda manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya sanya 'yan'uwantaka a tsakaninsu da shi, yayin da labarin hakan ya zo wa ziyad sai ya koma Kufa, kuma Mugira ya kiyaye wa ziyad wannan da gode masa. Sannan kuma sai ita ummu jamil ta zo wa Umar dan khaddabi wata shekara ya na can wurin aikin Hajji, kuma akwai Mugira a wurin, sai Umar ya ce masa: Shin ka san wannan matar ya kai Mugira? Sai ya ce: Na'am, wannan ita ce ummu kulsum 'yan Ali.

Sai Umar ya ce masa: Shin ka na nuna ba ka san komai ba ne, wallahi ba na tsammanin abubukrata ya yi karya a shedar da ya bayar kanka, kuma ban gan ka ba, har sai na ji tsoron kada a jefe ni da dutse daga sama.

 Ya ce: Sheikh abu Ishak shirazi ya fada a cikin babin adadin shedu a littafinsa muhazzab: Kuma mutum uku sun yi sheda kan Mugira wato abubukarta da nafi'u, da shibl dan ma'abad, ya ce: Amam sai ziyad ya ce: Na ga duwawu ya na yin sama ya yi kasa, da wani lumfashi da ya ke yin sama, da cinyoyi biyu kamar kunnunwa jaki, amam ban san abin da ya ke bayan nan ba. Sai Umar ya yi wa mutum uku bulala bai yi wa Mugira haddi ba.

Na ce: Malamai sun yi nuni ga maganar Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ga Umar cewa: Idan ka yi masa haddi to ka jefi sahibinka. Sai abu nasar assabbag ya ce: Wannan maganar ta na nufin cewa idan wata sheda ce to adadi ya cika, idan kuma ta farko ce to ka riga ka yi masa bulala a kanta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next