Umar da Ra'ayin Shari'a 2Sai Imam Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) ya fuskance shi ya na mai cewa: Ni ne wannnan da babata ta kira ni Haidar Kamar zakin jeji mai munin gani Ina cika muku awon kwanon nan na Sindara[8] Ya ce: Sai ya doki kan Marhab sai ya tsaga shi ya kashe shi, sai aka samu budi a hannunsa[9]. Daga ciki akwai yakin Silsila a yakin Wadir Raml, ita ma ta yi kama da yakin haibar yayin da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya aiki Abubakar da farko, sai rundunata ta dawo a rushe, sannan sai ya aika da Umar sai ya dawo da wadanda su ke tare shi haka nan, sai kuma ya aika Ali (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) bayansu sai Allah ya yi masa bude, ya dawo da ganimomi da ribatattu, godiya ta tabbata ga Allah, wannan kuma yakin sheikh mufid ya kawo shi dalla - dalla a littafinsa na Irshad, don haka sai a koma a duba. Yakin silsila ba shi ne yakin silasil ba wacce ta ke a shekarar bakwai bayan hijira, domin a wannan yakin na silasil an tura amru dan Aas ne a cikinsa, kuma a cikin rundunar akwai Abubakar da Umar da abu ubaida a cikin rundunar da su ke karkashinsa kamar yadda ya zo a tarihi gaba daya. Kuma a yakin an samu sabani tsakanin Umar dan khaddabi da amru dan aasi da hakim ya kawo a babin magazi a juzu'I na uku a littafin mustadarak[10] da isnadinsa zuwa abdullahi dan buraida daga babansa,. Ya ce: Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya aika maru dan aasi a yakin zatus salasil a cikinsu akwai Abubakar da Umar, yayin da su ka zo wurin yakin sai amru ya Umar ce su da su kunna wuta, sai Umar dan kahddabi ya ji haushi ya yi nufin hayayyake masa, sai Abubakar ya hana shi, sai ya ba shi labari cewa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) bai sanya si shugaba kansa ba sai saboda iliminsa da yaki, sai Umar ya nutsu. Bayan haka sai hakim ya ke cewa wannan hadisin ya na da isnadi mai karfi ingantacce, sai dai sheihaini ba su kawo shi ba, kuma zahabi ya kawo shi a talkhis ya kawo ingancinsa. Fadakarwa:
Akwai hikima ga Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) da ya kasance ya na da masaniya da ita da usulubi mai kyau cikin dora Ali da sanya shi jagora kan waninsa na daga sahabban farko da ta kasance cikin rayuwarsa. Daga ciki shi ne bai taba sanya wani jagora kan Ali ba, a yaki ne ko a rashin yaki ko a gida, amma babu wani wanda ba a sanya wani ya jagorance ba[11], Duba Amur dan aasi ya zama jagora kan Abubakar da Umar a yakin salasil kamar yadda ka ji, kuma manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi wafati alhalin a lokacin usama dan zaid duk da karancin shekarunsa shi ne jagora a kan Abubakar da Umar da abu ubaida da sauran su, kuma wannan sananne gun duk ma'abota tarihin musulunci.
|