Umar da Ra'ayin Shari'a 1Daga ciki, akwai gadon kaka namiji da 'yan'uwa
Baihaki ya kawo a littafin “Sunan†dinsa daga kuma littafin “shu’Abul iman†(wato; rassan imani) dukkaninsu[4] cewa Umar ya tambayai annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) game da gadon kaka tara da ‘yan’uwa sai ya ce masa: Me ye wannan tambayar taka ya Umar? Ina ganin har ka mutu ba ka gane wannan ba, mai ruwayar hadisi - Sa'id dan musayyib - ya ce: Har Umar ya mutu bai san wannan mas’alar ba. Na ce: Ya samu rudewa kan wannan mas’alar a lokacin halifancinsa har sai da ya yi wani hukunci kan ta da hukunci kala saba’in game da wannan. Ubaidatus salmani[5] ya ce: Na kiyaye kusan hukunci dari mabambanta daga Umar kan gadon kaka kawai. Daga Umar[6] ya ce: Ni ina hukunci game da kaka da hukunce - hukunce da na ke ta kokarin ganin na gane gaskiya. Daga karshe dai sai ya koma zuwa ga zaid dan sabit kan wannan lamarin mai wuyar sha’ani gare shi. Darik dan shihab azzuhuri[7] ya ce: Umar ya kasance ya yi hukunci game da gadon kaka tare da ‘yan’uwa da hukunci mai sabawa, sannan sai ya tara sahabbai ya riki wani takarda don ya rubuta kan haka, su kuma su na ganin ya sanya shi uba kawai, sai wata macijiya ta fito sai su ka waste, sia ya ce: Da Allah ya na son ya zartar da shi da ya zartar da shi, sannan sai ya ta fi gidan zaid dan sabit sai ya ce masa: Na zo maka ne game da lamarin kaka, ina ganin in sanya shi uba, sai zaid dan sabit ya ce: Ni ba na tare da kai a ra’ayin sanya shi uba, sai Umar ya fita ya na mai fushi har sai da ya aika masa a wani lokaci, sai zaid ya rubuta masa ra’ayinsa kan hakan a wani dan guntun fata, yayin da wannan rubutun na zaid ya zo wa Umar sai ya yi wa mutane huduba sannan ya karanta guntun fatar gare su, sannan sai ya ce: Zaid ya yi wata magana kan kaka da na riga na zartar da shi (maganar ta zaid). Daga ciki, akwai rabon tarayya da aka sani da himariyya
Bayani takaitacce na wannan gadon shi ne idan mace ta mutu ta bar miji da uwa, da ‘yan’uwa biyu na wurin uwa kawai ban da na wurin uba, da kuma wasu ‘yan’uwa biyu shakikai (uwa da uba daya). Wannan ya faru a lokacin halifa na biyu sai matar ta kai wannan mas’ala gun sa, sai ya yi hukunci da: A mas’ala ta farko a bawa miji rabonsa wato rabi, a ba wa babarta rabonta wato sudusi, sannan sai a ba wa ‘yan’uwanta na wurin uwa sulusi kowanne ya samu sudusin dukiya, sai dukiya ta cika, ya kuma jefar da ‘yan’uwanta shakikai (wadanda su ke uwa da uba daya). A na biyu kuwa; da ya so ya yi wannan hukuncin sai daya daga cikinsu ya ce: A sanya cewa babanmu ya kasance jaki ne, to a yi tarayya da mu tabangaren kusancinmu da uwarmu mana, sai ya yi tarayya da su a raba sulusi ga ‘yan’uwan su hudu duka da daidaito. Sai wani mutum ya ce: Ai a shekara kaza ba ka sanya da su ba. Sai Umar ya ce: Waccan ta na nan kan abin da mu ka hukunta a lokacin, wannan kuma ta na kan abin da mu ka ambata a yanzu[8]. An san wannnan mas’alar da sunan rabon gadon himariyya, saoda wannan mtumin da ya ke cewa: A sanya cewa babanmu jaki ne, wani lokaci kuwa ana kiran ta da hajariyya, da yamiyya, yayin da wasu daga cikinsu su ka ruwaito cewa ya ce ne: Sanya cewa babanmu ya kasance dutse ne da aka jefar a yammi (tekun maliya), kuma ana kiran ta da umariyya saboda sabawar maganganun Umar biyu a cikinta, ana kuma ce mata mushtaraka (ta tarayya)[9], kuma ta na daga cikin mas’aloli sanannu gun malaman mazhaba hudu, kuma sun yi sabani a kanta, abuhanifa da sahibansa biyu, da Ahmad dan Hambal, da zufar, da Ibn abi laila, su na ganin haramcin kason ga ‘yan’uwa shakikai biyu bisa abin da Umar ya hukunta da farko, sabanin maliku da shafi’I su su na ganin su yi tarayya a cikin sulusi su duka bisa hukuncin Umar na karshe. Ammam imaman shiriya ahlul bait (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare Shi) haka nan malamai mabiyansu kamar yadda mu ka kawo a baya ba sa sanya wa wani dabaka ta kasa gado, tare da samun dabaka ta sama ko da mutum daya ne kuwa, uwa ta na daga cikin dabaka ta farko bisa ittifakin su, amma ‘yan’uwa su na daga dabaka ta biyu ne, kamar yadda ya ke a masl’alar cikin fikihu, don haka a gun su sai miji ya dauki kasonsa shi ne rabi, saura kuwa sai uwa ta dauke su bisa kaso da raddi, don haka babu wani daga cikin ‘yan’uwa da ya ke da wani abu na kaso.
|