Umar da Ra'ayin Shari'a 1Sunnoni da aka rauwaito masu yawa a cikin ingantattun littafai ne su ka zo, kuma wannan mas’ala dukkan la’umma ta yi ittafikai a kanta, kuma ba a karbo wani sabani ba daga wani sai daga Umar dan Khaddabi, kuma shahararriyar magana daga gare shi[15] shi ne farilla ta na faduwa ga wanda bai samu ruwa ba, har sai ya samu. Hakika Buhari da Muslim sun fitar a babin taimama a littattafansu daga Sa'id dan Abdurrahman dan Abzi daga babansa cewa wani mutum ya zo wa Umar sai ya ce: Ni ina da janaba ban samu ruwa ba. Sai ya ce: Kada ka yi salla - kuma Ammar dan Yasir ya kasance a wurinsa - sai Ammar ya ce: Shin ka tuna ya sarkin muminai yayin da ni da kai mun kasacne a wani yaki sai mu ka yi janaba sai ba mu samu ruwa ba, amma kai ba ka yi salla ba, amma ni sai na yi birgima da turbaya na yi salla, sai annabi (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Kawai ya ishe ka ka buga kasa da hannayenka, sannan sai ka busa, sai ka shafa fuskarka da tafukanka da su. Sai Umar ya ce: Ka ji tsoron Allah ya Ammar. Sai Ammar ya ce: Idan ka na so ba zan gaya wa wani shi ba[16]!! Sai Umar ya ce: Za mu dora maka nauyin abin da ka dauka. A nan ya tuke da lafazin Muslim. Ana cewa Ibn msa’ud ya karkata zuwa ga ra’ayin Umar a wannan mas’alar: Yayin da buhari da waninsa na ma’abota ingantattun littafa da sauran littattan Sunan da lafazin buhari su ka kawo ta hanyar Shafik dan Salama[17], ya ce: Na kasance gun Abdullah dan mas’ud da Abu Musa al’ash’ari, sai abu musa ya ce masa: Ya kai baban abdurrahma, idan baligi ya yi janaba bai masu ruwa ba me zai yi? Sai abdullahi ya ce: Ba zai yi salla ba har sai ya samu ruwa. Sai Abu Musa ya ce: Yaya za ka yi da maganar Ammar yayin da Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce masa: Ya isar maka…? Sai ya ce: Ba ka ga Umar bai gamsu da wannan ba. Sai Abu Musa ya ce: Bari maganar Ammar! Amma yaya za ka yi da wannan ayar - sai ya karata ayar Surar Ma’ida - ya ce: Sai Abdullahi ya rasa me zai ce…†hadisi. Na ce: Ibn Mas’ud a wannan maganar tasa tare da Abu Musa ya kasance ya na mai yin takiyya ne saboda tsoron Umar da sahibinsa Abu Musa, kuma babu wani kokwanto kan hakan, Allah ne mafi sani. Daga Ciki, akwai Nafila Raka’a Biyu Bayan La’asar
Muslim ya kawo a cikin littafinsa[18] daga Urwa dan Zubair daga babansa daga Aisha ta ce: Manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) bai bar yin raka’a biyu bayan la’asar ba guna da rana daya. Haka nan ya karbo daga Abdurrahman dan Al’Aswad daga babansa, daga ai’sha ta ce: Salla biyu manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) bai taba barin su ba a dakina a boye ko a bayyane, raka’a biyu kafin alfijir, da raka’a biyu bayan la’asar. Kuma ya karbo wata ruwayar daga Al’Aswad da Masruk, sun ce: Mun shaida cewa A’isha ta ce: Bai taba kasancewa ranar kwanansa ba guna sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya sallace su a dakina, ta na nufin raka’a biyu bayan la’asar. Haka nan ya zo a lafazinsa. Sai dai Umar dan khaddabi ya kasane ya na hana yin su, kuma ya na dukan duk wanda ya ke yin su daga musulmi.
|