Umar da Ra'ayin Shari'a 1* Waye zai isar da sakona ga ubangiji mai tausayi Cewa ni bar yin azumin watan azumi * Ka gaya wa Allah ya hana ni abin shana Ka gaya wa Allah ya hana ni abincina Sai wannan labarin ya je kunnen manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) sai ya futo cikin fushi ya na jan mayafinsa, sai ya daga wani abu da ya ke hannunsa ya doki kan Umar da shi, sai ya ce: Ina neman tsarin Allah daga fushinsa da fushin manzonsa (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), sai Allah ya saukar da ayar nan da fadinsa: "Kawai shedan ya na son ya haifar da gaba da kiyayya tsakaninku ne a cikin giya da caca, kuma ya kange ku daga ambaton Allah daga kuma yin salla, shin za ku bari kuwa" Ma'ida: 91. Sai Umar ya ce: Mun bari hakan! mun bari haka nan![44]. Daga ciki; abin da ya kasance ranar da aka hadu tsakanin jama'a biu da yakki na hanin kashe Abbas da wanisa, daga wadanda mushrikai su ka tislasta musu fitowa tare da su
Wannan kuwa ya faru ne yayin da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya gaya wa sahabbansa a ranar Badar yayin da yaki ya yi zafmi cewa: Na san akwai wasu mutane daga BAnu hashi da wasunsu da aka fito da su bisa tilas, ba su bukatar yakar mu, duk wanda ya hadu da wani daga Banu hashim to kada ya kashe shi, kuma duk wanda ya hadu da Abul Bukhtari dan hisham dan alharis dan asad to kada ya kashe shi, duk wanda ya hadu da Abbas dan abdul mudallib ammin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) to kada ya kashe shi[45], domin ya fito bisa tilas ne. Ka ga manzon Allah ya hana kashe babn hashi gaba daya, sannan sai ya hana kashe amminsa Abbas musamman don karffa hanin kashe shi, da tsanantawa kan hakan, amma yayin da aka kama Abbas sai amanzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya kwana bai yi bacci ba. Sai sahabasa su ka ce masa: - kamar yadda duk masu ruwayar tarihi su ka kawo a game da yakin bada - Me ya hana ka uyin bacci? Sai ya ce: Na ji gumjin Abbas ammina a cikin daurin da aka yi masa, sai ya hana ni yin bacci, sai su ka tashi su ka sake shi, sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi bacci yayin nana. Daga yahaya dan abu kasir: Yayin da ya kasance ranar bada, sai musulmi su ka ribace mushrikai saba'in, ya kasance Abbas ammain amanozn Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya na daga cikin wadanda aka ribace, sai Umar ya jibanci daure shi, sai Abbas ya ce: Amma wallahi ya kai Umar ba komai ne ya sanya ka yi mini wannan daurein ba, sai marin ka da na yi saboda kariya ga manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka). Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya rika jin kugin abbasa sai ya kasa yin cbacci. Sai su ka ce: Ya ma'aikin Allah me ya hana ka yin bacci? Sai manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya ce: Yaya kuwa zan yi bacci alhalin ina jin kougin ammina Abbas. Sai ansar su ka zo su ka kwance shi… Hadisi[46]. Sahabban manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) muhajirai da ansar da wasunsu dukkansu sun san abin da Abbas ya ke da shi na falala da matsayin gun manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), da son lafiya da girmamawa gare shi. Yayin da maganar Abu huzaifa dan utuba dan rabi'a dan abdus shams ta zo masa ya kasance ya na tare da shi a badar - yayin da ya ce: Yanzu za mu kashe iyayenmu da 'ya'yanmu da 'yan uwanmu mu bar Abbas, wallahi idan na hadu da shi sai na yi masa takunkumi da takobi, sai wannan magana ta bata wa manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) rai game da abu huzaifa, sai ya nemi taimako da Umar ya na gaya masa don ya tayar da bangarencinsa cewa: Yanzu za a sari fuskar ammin manzon Allah da takobi? Umar ya ce: Wallahi ita ce ranar farko da manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya yi mini kinaya da abu hafs[47], sai bayan yaki ya gama, Allah ya bayar da nasara ga bawansa, ya taimaki rundunarsa, ya kashe dawagiti saba'in, ya ribace saba'in, har ak zo da su a daure, sai abu hafs ya tashi ya na tunzurawa don kashe su da mafi tsananin harshe ya na mai cewa: Ya ma'aikin Allah, sun karyata ka, sun fitar da kai, sun yake ka, ka ba ni dama in kama wane in sare wuyansa, ka ba wa Ali dama ya sare wuyan dan'uwansa akil, ka ba wa hamza dama ya sare wuyan dan'uwansa abbasa. Na ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Abbas ko akil ba su kasacne cikin wadanda su ka karyata Allah da manzon sawa, kuma ba sa cikin wadanda su ka fitar da shi, ko su ka cutar da shi, sun kasance tare da shi a cikin zazar filin nan da aka tsare su aka sanya musu takunkumi tare da shi, su ka sha wahala taer da shi a cikin wannan bala'o'in, kuma an fito da su don yin yakin badar ne bisa tisal da fadin manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka), kuma manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) ya hana kashe su a lokacin tsakiyar yaki, to yaya kuwa za a kashe su bayan su na ribatattun yaki?! Idan kuwa nishin abbasa ya hana manzon Allah (Mai Amincin Allah ya Kara tabbata Gare shi da Alayensa Tsarkaka) yin bacci, yaya kuwa ka ke tsammanin zai kasacne idan aka kashe shi ba tare da wani dalili kan hakan ba. Abbas ya kasacne daga wadanda su ka kasance musulmi tun kafin hakan, kuma ya boye musuluncin ne saboda wata hikima da Allah da manzonsa su ke da yarda cikinta, kuma akwai maslahar al'umma tare da hakan[48].
|