Dalilin Shi'ancin FarisawaKuma duk wani mai bincike ya san cewa kowace al’umma tana da wani abu da ta hadu da wata al’ummar a kansa a wani ra’ayi ko wata mas’ala amma duk da haka wannan ba ya sanya a ce musu abu guda. Mu fara da Ahmad Amin kansa mu dora masa ra’ayinsa a kansa zamu ga dalilin da ya dora wa Shi'a shi ma yana hawa kansa; idan mun duba zamu ga yana tafiya a Mas’alar Jabar da Zabi malaman Falsafa na Yunan sun yi magana kanta kafin musulmi su yi magana game da ita, kuma Saryaniyawa sun samu wannan daga garesu ne, kuma Zardashtiyyun su ma sun yi magana kanta kamar yadda Kiristoci suka yi, sannan sai Musulmi[8]. Don haka bisa dogaro da maganar Ahmad Amin muna iya cewa ke nan musulmi sun zamo Nasara saboda sun yi ittifaki da Nasara a kan wannan ra’ayi na Jabar, idan kuwa ba haka ba, mene ne dalilin Ahmad Amin na ganin Shi'a cewa Farisawa ne saboda kawai sun hadu da su kan maganar Hakkin Allah madaukaki?. Amma abu na biyu na da’awar cewa dukkan kowanne daga Farisawa da kuma Shi'a suna ganin jagoranci a matsayin gado ne to wannan batacce ne game da Shi'a, domin Shi'a ba sa ganin jagoranci gado ne, suna ganin al’amari ne na nassi daga Allah (s.w.t) ta hannun Annabi (s.a.w) ko Imami (a.s), kuma littattafan Shi'a cike suke da wannan al’amari[9]. Kuma mas’alar nassin A dunkule dai wannan muhawara da ire-irenta tana yi mana bayanin matsayin Shi'a kan al’amarin Imamanci, kuma ita nassi ce ba gado ba, don haka a ina ne mustashrikai da dalibansu suka samu wannan magana ta gado idan dai ba rashin sanin mene ne Shi’anci ba ko kuma son neman karkatar da gaskiya da son rai. 3- Al’amari na uku: Shi ne shigar Farisawa musulunci domin son su rusa shi sannan kuma su tabbatar da hadafinsu da shigar da ra’ayin kakanninsu; wannan ra’ayi dai batacce ne, kuma muna iya cewa kamar haka: Na farko: Littattafansu masu kariya ga musulunci da masallatansu da kuma cibiyoyinsu na addini da jihadinsu a tafarkin Allah duk wannan yana nuna mana karyar wannan da’awar da ake yi.
|