Dalilin Shi'ancin Farisawa
Dalilan Shigar Farisawa Cikin Shi’anci
1- Al’amari Na Farko: Surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa cewa ya auri â€کyar sarki Yazdajir kuma shi daya ne daga sarakunan sasaniyawa kuma sunanta Shahezanan, sai tahaifa masa Aliyyu dan husani wanda gadon sarakuna ya taru a cikinsa, da kuma siffar Imamanci daga iyayensa maza, har ma Abul Aswad Addu’ali yana fada game da shi: Hakika abin Shi ne mafi girman wanda aka A game da haka ne Sumaira Allaisi take karawa 2- Al’amari Na Biyu: Kusantar ra’ayoyi tsakanin Shi'a da Farisawa; daga wannan akwai batun hakkin Ubangiji, don haka kowa yana ganin hakkin Allah yana nan ga wanda ya zaba na daga jagorori, shi bafarise yana ganin wannan hakki ga sarakunan Farisawa, shi kuma dan Shi'a yana ganin wannan ga jagorrorinsa, wannan kuwa koda wasu suna ganin cewa Shi'a sun tasirantu da Farisawa ne, kuma tun da dai Shi’anci ya rigayi shigar Farisawa cikinsa, kuma tun da dai wadanda suka shiga cikinsa na daga Shi'a dukkaninsu Larabawa ne kamar yadda muka tabbatar da hakan a abin da ya rigaya, kuma tun da dai nazarin Shi'a game da Imami bai saba ba kamar yadda yake gun zurara daga abin da yake gun Ammar da Abuzar to don haka muna iya cewa nazarin nan na hakkin Allah da Shi'a suka yi ittafaki da Farisawa a kansa bai kasance sakamakon tasirantuwa da ra’ayoyin Farisawa ba ne, wanda yake kunshe da imanin Shi'a da cewa Imam Ali (a.s) wasiyyin Annabi (s.a.w) ne, kuma shi ne wanda aka yi nassi da bin sa, kuma da yawa daga mustashrikai sun saba da fadin irin wannan kusanci da su da dalibansu:
|