Dalilin Shi'ancin Farisawa4- Iyakance hakikanin sunnanci daga wannan al’amarin da dalilai da aka kawo daga littafin Sunna; Amsa A Kan Dalilan Shigar Farisanci Shi’anci
1- Al’mari Na Farko: Surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa; Yana daga cikin abubuwan da kowa ya yarda da su shi ne: Ka’idar nan ta cewa hukuncin abubuwan da suke iri daya A nan ne muke tambaya cewa: Idan dai surukuta ita ce dalili to don me ba zamu ga Farisawa sun karkata ga surukansu na Abdullahi dan Umar da Muhammad dan Abubakar ba!? Kuma kowanne daga cikinsu shi Muhammad da Abdullahi â€کya’yan halifofi ne, kamar yadda Husain yake dan halifa ne. Hada da cewa dukkansu kowanne Yazid dan Walid dan Abdulmalik, da babarsa Shafarand â€کyar Fairuz dan Yazdajir, da Marwan dan Muhammad karshen halifofin Banu Umayya wanda babarsa ita baiwa ce daga Kurdawan Iran, don me ba ma ganin irin wannan dalili a kan al’amarinsu[7], kuma a bisa akasin haka don me ya sa Larabawa su ba sa karkata ga Ahlu-baiti (a.s) ai iyayensu Larabawa ne, yayin da muke ganin wasu jama’a daga Larabawa sun zamanto makiya ga Ahlu-baiti (a.s); wannan tambaya ce ga wadannan hankulan da suke rubutu amma ba sa tunani. 2- Al’amari Na Biyu: Kusancin Ra’ayi Tsakanin Shi'a da Farisawa: Kowanne daga cikin masu ra’ayin Hakkin Allah suna cewa akwai gado kuma babu batun zabi a jagoranci, wannan kuma ya tababatar da abubuwa biyu da suka sanya dalilin shiga Shi’anci: Wannan al’amari ina ganin duk wanda ba ya girmama hankalinsa shi ne zai kawo shi, domin yaushe ne dai kawai don kun yi tarayya da mutum a wani abu na akidu sai a samu haduwa a akida daya ya jefar da tasa ya yi riko da taka. (Kamar yadda su masu sukan suke kawo cewa Farisawa sun yi wurgi da ta su akida suka shiga shi'anci saboda kawai sun yi tarayya da shi a wani abu! Wannan wace irin wauta ce? Yaushe ne wani mai hankali yake yin hakan?)
|