Dalilin Shi'ancin FarisawaMuhammad Abu Zuhra yana cewa: Kuma wasu daga sashen malamai daga cikinsu akwai Duzi mustashriki ya tabbatar da cewa asalin mazhabar Shi’anci wani tunani ne daga Farisanci yayin da Larabawa suna da tunanin zabe ne, Farisawa kuma suna da tunanin mulki ne da gado, ba su san wani abu da ma’anar gado ba, har ya ce; Shi'a sun tasirantu da tunanin Farisanci game da mulki da gado[2]. Haka nan Ahmad Amin da wasu mustashrikai suka tafi a 3- Al’amari Na Uku: Wasu masu kin shi'ancin suna cewa: Shigar Farisawa Shi'anci ya kasance da nufin rusa muslunci ne da boyewa karkashin son Ahlul-baiti (a.s), sannan sai aka shigo da wadannan ra’ayoyin masu rusa musulunci kamar fadin batun Wasiyya, Raja'a, da Mahadi (a.s) da sauransu. A kan haka ne Ahmad Amin yake cewa: A bisa gaskiya Shi’anci ya kasance mafaka ce da dukkan wanda yake son rusa musulunci yake fakewa da shi don gaba ko mugun kulli, haka nan dukkan wanda yake son shigar da koyarwar iyayensa na yahudanci da kiristanci da zardashtanci da indiyanci, da dukkan wanda yake son â€کyancin kasarsa da fita daga masarautarsa sun labe karkashin son Ahlu-baitii[4] ne. Ina fatan mu duba irin wadannan maganganu da muryoyi na kiyayya a Saoba kuma mu dan yi karin haske a 1- Raddi 2- Iyakance hakikanin Shi’anci a bisa kabilanci 3- Iyakance hakikanin Shi’anci a tunani
|