Hakikar Shi'anciA bisa misalin ruwayoyin da suka zo game da nunin fifikon Ali (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w) shin suna bayani ne ta yadda zai wajabta a kan musulumi su yi riko da imamancinsa ta fuskancin wasiyya gareshi da halifanci, kuma idan haka ne; shin wannan jagorancin ya tsaya ne gun abubuwan da suka shafi jagoranci ko kuma dole ne Imami (a.s) ya kasance yana da fifiko a komai kamar ya kasance shi ne mafi ilimin mutane, mafi karfinsu, mafi adalcin mutane, haka nan ma abin da ya shafi isma da sauransu. To dukkan wannan al’amuran suna shiga cikin lamarin jagoranci halifancin Annabi, ba wasu al’amura ba ne da suka dadu a kan asalin wannan lamarin, sai dai sun bubbugo ne daga ci gaban tunani da kuma daduwar yawan masu karbar mazhabar, da yawan mas'aloli da tambayoyi da ake tayarwa kan lamarin imamanci wato halifancin Annabi (s.a.w). 2- Irin wannan ci gaban kamar irin ci gaban zamani ne, don haka ne ma musulunci ya samu ci gabansa tare da samun tofuwa da bullar wasu mazhabobi. Musulmi tun farkon samuwarsu sun yi imani da Allah da samuwarsa da kadaitakarsa, da siffantuwarsa da siffofin kamala da tsarkakarsa daga siffofin tawaya, kuma amma duk wannan a dukkule ne. Amma yayin da fagen tunani ya fadada, kuma duniyar musulmi ta bude wa al’umma da al’adu mabambanta, sai ga mas’aloli suna kunno kai, sai musulmi suka koma wa abin da suka yi imani da shi a dunkule suna masu gini a kan dunkulallun bayanansa a takaice, suna fasa su dalla-dalla al'amarin da ya haifar da fikirori daban-daban, kuma wannan ya faru game da imaninsu ga mahaliccin komai: Aka samu jayayya game da sabuban halitta a game da siffar halittawa, wanda a ganin wasu wannan yana iya kai wa ga kididdigar mahalicci, ko kuma wannan yana rushe kadaitakar Allah a matsayinsa na mahallicci: Domin Allah madaukaki yana da tasirin da halittu ba su da shi, kuma dukkan abin da yake ga ababan halitta ta wata fuska ne, kuma wannan ba ya rusa cewa Allah madaukaki shi ne mafificin masu halittawa. Sai wannan mas’ala ta haifar da mas’alar ayyukan bayi, da kuma alkanta wannan da mas’alar zabi ko tilasci a cikin ayyukan bayi. Wani misalin shi ne: Imanin da musulmi suke da shi tun lokacin da suka samu hujjar da suke da ita ta ayoyin Kur'ani mai girma, sai wannan ya sanya su jayayya game da zahirin wasu daga ayoyin Kur'ani domin wannan yana nufin jingina abin da bai inganta ba zuwa ga Allah madaukaki, wannan irin mas'alar ta hada da irin fadin Allah madaukaki cewa: "Wasu fusaku a wannan rana masu haske ne, suna masu duba zuwa ga Ubangijinsu". Alkiyama: 22. Yayin da Ahlussunna suka tafi a kan cewa zai yiwu a ga Allah madaukaki a ranar kiyama da idanuwa kuru-kuru, dogaro da zahirin aya, su kuma malaman imamiyya (Shi'a) suka tafi a kan cewa mustahili ne a ga Allah domin wannan yana nufin yiwuwar jiki ga Allah (s.w.t), daga karshe kuma a samu hauhawar sassa ga Allah sannan sai kuma bukatuwa, sai faruwa gareshi, daga karshe ke nan sai a kore wa Allah Ubangijintaka, don haka ne ma suka tafi a kan cewa fassara kalmar "Nazar" a wannan aya tana nufin sauraron rahama, ba ganin Ubangiji ba. Kamar yadda ake yin amfani da ita a harshen Larabci da wannan ma’ana yayin da wani zai ce da wani ina sauraronka, kuma Kur'ani ya sauka ne da harshen Larabci kamar yadda suke magana a cikin muhawarorinsu. Wannan ke nan hada da cewa Ubangiji madaukaki ya danganta wannan kalma zuwa ga fusaku da cewa su ne aka jinginawa Haka nan wani misali da zan iya kawowa shi ne na yawaitar al’amuran musulunci fiye da yadda yake a zamanin farko, musulmi sun yi imani da cewa Allah ba ya aikata wasa kuma zahirin ayoyin Kur'ani sun zo suna karfafa hakan, ya zo a cikin fadinsa madaukaki: "Wannan da ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarrabe ku" surar Malik: 2. Ya zo da fadinsa cewa: "Ba mu halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu suna masu wasa ba" Dukhan: 38. Amma duk da hakan musulmi sun yi jayayya bayan hakan a kan cewa shin ayyukan Allah suna da hadafi wanan kuma yana nufin tawaya ga Allah (s.w.t) domin dukkan mai aikin da yake da hadafi to yana bukatar mai samarwa, ko kuma ayyukansa ba su da hadafi, wannan kuma yana lizimtar cewa ayyukansa wasanni ne, Allah (s.w.t) kuwa ya barranta daga hakan. Sai ahlussunna suka tafi a kan cewa ayyukansa ba su da hadafi, sai imamiyya suka tafi a kan cewa suna da hadafi ba tare da wannan ya lizimta wa Allah wani mai samarwa gareshi ba, wannan kuwa domin amfanin yana komawa ne zuwa ga bayi kansu, don haka zai yiwu a hada tsakanin wadannan al’amura biyu ke nan, sai ya kasance amfanin bayi da kuma kasancewar Allah ba ya wasa, kuma ba ya bukatuwa zuwa ga komai. Duk da wadannan abubwan da muka fada ba zai yiwu ba a ce; akidun musulmi sun fi yawa fiye da yadda suke a da can farkon musulunci, abin da ya faru shi ne musulmi sun dada yalwatawa cikin sharhin al’amura a dunkule yayin da suka bukaci hakan sakamakon haduwar su da sauran al’adu da fikirori iri-iri. Musulmi a farkon musulunci da musulmi a wannan zamanin namu dukkansu suna da madogara daya ne wato; Littafi da Sunna, samma abin da ya gabata a dunkule ne sai aka bukaci bayani dalla-dalla saboda samuwar bukatuwa zuwa ga hakan alhalin da can babu ita a farkon musulunci, don haka ci gaban da shi'anci ya samu irin wannan ne da ya faru a cikin musuluncin kansa, kuma shi a bisa hakika da wannan ma’anar ba shi da wata jayayya a kai. Amma faruwar sababbin ra’ayoyi wadanda suke nesa da musulunci babu wannan a cikin shi'anci, domin duk wani abu da musulunci yake kin sa, to bisa tabbas Shi’anci yana kin sa, hakika dukkan abin da ya faru a musulunci kamar yadda muka fada din nan babu wani tawaya da yake haifarwa ga akidun jama’un musulmi, kuma idan abin da ya faru a Shi’anci na ci gaba kamar abin da ya faru ne a musulunci to mene ne yake haifar da wata matsala a akida kuma ya kawo wasu matsaloli da ba su da wata madafa, har ake jifan Shi'a da su?. 3- Idan ma mun sauko mun kaddara shigar wani abu a cikin Shi’anci kamar yadda wasu suke son tabbatarwa haka nan babu wani dalili to irin wannan kaddarawar tunanin Shi’anci yana kin sa idan ya kasance ba ya daidai da abin da yake cikin littafin Allah da sunnar annabinsa (s.a.w) da kuma tsarin musulunci gaba daya, irin wannan kaddarawar ra’ayi ne da yake komawa kan mai shi, kuma duk abin da ba cikin musulunci yake ba to babu shi a Shi’anci da tabbacin cewa Shi’anci fikira ce da ta zo daga Ahlu-baiti (a.s) kuma su ne daidai da Kur'ani kuma su kamar jirgin Nuhu (a.s) ne, don haka ne wanda yake danganta wani abu mummuna ga Shi’anci ya samu cakude ne tsakanin Shi’anci da kuma â€کyan Shi'a, kuma da yawa wanda ake cewa da shi dan Shi'a amma shi'ancin yana kin sa a bisa tsarinsa wanda abu ne da zamu kawo shi nan gaba, sha’anin wannan shi ne kamar sha’anin sunnanci ne wanda yake kore wasu masu rabuwa da shi wadanda karkacewarsu ta tabbata daga tsarin tafarkin musulunci, kuma samuwar irinsu ba ya cutar da ahlussunna, kuma wannan ba ya hana a kira su da Sunan da ake gaya wa ahlussunna gaba daya. A mafi munin kaddarawa idan an samu wasu karin mas’aloli a cikin kowace irin wace mazhaba ce, kuma ya kasance dadi a kan asalinsa kamar yadda yake an kaddara kuma an dauka haka ne, to hakan ba ya iya haifar da wani musun abubuwan da suke laruri na addini ga mai wannan akida, kuma ba ya kaiwa ga ridda ko karkacewa. Sannan irin wannan ba ya sanya jifa da Yaushe ne fadin wasiyya ga Ali (a.s) a bisa misali da cewa kowane Annabi (a.s) yana da wasiyyi, kuma wasiyyai (a.s) dole su kasance ma’asumai ne domin a samu tabbatar hadafin kafa su jagorori ga al’umma su tabbata da kuma imani da cewa Imam mahadi (a.s) rayayye ne, da makamancin wannan na daga akidoji, yaushe ya kasance fita daga addini kuma ya kai ga hari da jifa da kalmomi munana maras dalili wanda mutanen zamaninmu na yau ba su gushe ba suna bin marigayansu ba tare da sanin asalin wannan sukan ya bayyana ba, kuma ba a yi tattaunawa a kai ba domin warware mas’alar. Amfani da dukkan karfi a fagen soki burutsu ba shi da wani amafani ko kadan, hada da cewa zai iya yiwuwa a yi amfani da wannan karfin a wajan da ya dace domin kawo hadin kai da kuma kawar da duk wani abu da ya gurbata lamarin musulmi, da kuma tsaftace yanayin musulunci daga gaba da kiyayya da mugun kuduri da kulli wanda ba ya amfanar da kowa sai makiya musulunci. Kuma duk wadanda suke iza wutar kawo rarraba da gaba tsakanin musulmi to mutane ne da suke nesa da musulunci kuma ba su da nisa da shubuhohi da rudu, musamman irin wadannan al’amuran yana zama wajibi ne su kasance sun takaita da malamai ne kawai, kada ta sauko a tsaka-tsakin mutane balle taci barkatai din su. Wannan kuwa domin malamai suna da wata kariya da take hana su nisanta daga kallon hadarin kaji, da harara, da kuma gabar jahiliyya, kamar yadda muke iya gani cewa kumajin kabilanci da bangaranci a tunanina ya fi hadari a kan dan Adam fiye da makamin kare dangi. Haka nan kuma a tarihin musulmi an samu sabani da ya kasance kuma har yanzu yana nan yana shake da bakin ciki a bakin duk wani mumini mai imani da Allah (s.w.t) da addininsa da dukkan hadafin sakon sama na Ubangiji madaukaki wanda yake yana daga hadafinsa shi ne sanya ruhin mutumtaka da â€کyan’adamtaka a cikin dukkan wani loko na rayuwar dan Adam. [1] Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
|