Hakikar Shi'anci



Kuma haka nan an nakalto wannan ma’anar ta Shi’anci daga Mustapha Asshaibi a littafinsa na "Sila".

3- Shahristani a cikin "Milal wan Nahal" ya ce: "Shi'a su ne wadanda suka bi bayan Ali (a.s) kuma suka yi furuci da jagorancinsa da halifancinsa a nassi da wasiyya ko bayayyananne ko boyayye kuma suka yi imani da cewa jagoranci ba ya fita daga ’ya’yansa, idan kuwa ya fita daga hannunsu to sai dai da ta hanyar zaluntarsu da waninsu ya yi ko kuma da takiyya daga garesu".

4- Nubkhati a littafinsa na firak ya ce: "Shi'a su ne jama’ar Ali (a.s) da ake ce musu Shi'ar Ali a zamanin Annabi (s.a.w) da kuma duk wanda ya tafi a kan son Ali (a.s).

5- Muhammad Farid Wajdi a littafinsa na "Da’iratul Ma’ariful Karnil Ishrin" ya ce: Shi'a su ne wadanda suka yi biyayya ga Ali a game da jagorancinsa kuma suka yi imani da cewa jagoranci na â€کya’yansa ne kuma ba ya fita daga hannunsu kuma suka ce su imaman ma’asumai ne daga manya da kanana zunubbai kuma suka yi furuci da wilaya (son Ali da jibinta lamari gareshi) da barranta (kin azzalumi da gaba da makiyan Allah da Manzo da imamai) a zance da aiki sai dai alokacin takiyya yayin da suka ji tsoron riko da kamun azzalumi".

Wadannan su ne misalai na bayani da zamu gabatar domin ka san mene ne Shi’anci a ra’ayin malamai masana masu bincike, kuma da wannan muna iya ganin wasu sun hada:

Cewa Shi'a suna gabatar da Imam Ali da fifita shi a kan wanisa na sahabbai saboda samun nassin shari'a a kan hakan ko kuma samun wata siffa da ya kebanta da ita kuma babu ita ga waninsa, kuma a fili yake cewa Shi’anci shi ne lizimtar fadin imamancin (jagorancin) Imam Ali da zuriyarsa da kuma fifita ta a kan waninta saboda nassin shari'a da Shi'a suke da shi a kan hakan, kuma muna iya fahimtar abubuwa biyu game da hakan:

Na farko: Imamanci jagoranci ne na nassin shari'a, kuma Imamai (a.s) sun ci gaba da isar da sakon Annabi (s.a.w) ne kuma duk abin da annabta take da shi na hakki kamar biyayya da isma in banda wahayi to yana tare da imamanci.

Na biyu: Imamanci ba ya yiwuwa da zabe domin Allah ne yake ayyana wanda ya so, kuma an yi nassi ta hanyar Annabi (s.a.w) da biyayya ga jagorancin Imam Ali (a.s) bayansa, kuma ya zabe shi da siffofi da yake da su da babu wani mai su.

Amma dadi a kan abin da muka fada wanda ya zo a cikin wadannan bayanai da muka kawo wadanda ana samun su a cikin wasu llittattafai da nassi wanda muna iya cewa ya hada da asasin mazhaba ne ko na musulunci kamar yadda zaka gani a bayanai da zasu zo nan gaba, kuma hadafin yin wannan bayanai shi ne domin mu yi karin haske kan abin da malamai masana suka kawo ne game da Shi'a da akidojinsu.

Irin wadannan ra’ayoyi da zamu kawo suna neman su sanya alaka tsakanin Shi’anci da yahudanci ko kiristanci ko zindikanci da kokarin jingina Shi’anci da wasu jama’a daban. Wadannan masu kawo irin wadannan ba komai suke nufi da wannan ba sai kokarin nuna cewa Shi’anci bai samu tofuwa ba kamar yadda sauran mazhabobi suka tofo. Kuma zamu yi maka bayanin wadannan ra’ayoyi da suke nuna Shi’anci da wata ma’ana maras inganci domin bata Sunan Shi’anci. Sannan kuma bayan kawo wadannan ra’ayoyi na masu gaba da Shi’anci sai in yi nawa bayani a kai.



back 1 2 3 4 5 6 next