Hakikar Shi'anci



Sheikh Wa'ili (r)

Gabatarwar Bugu Na Biyu

Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugbanmu Muhammad da alayensa tsarkaka da sahabbansa da wanda ya bi su da kyautatawa, bayan haka:

Wannan dan littafin ya kasance mai kayatarwa gun masu karatu duk da kuwa ya kasance takaitacce, wannan kuwa ba domin komai ba sai domin irin tsarin da na bi ne wajen rubuta shi ya kasance ya fi littafin kansa kyau, domin idan mun duba zamu ga shi littafin ba shi da wani girma sosai ta yadda zai kasance ya yi wani fice ta wannan fuskacin, sai dai zamu iya ganin sa bai wuce wasu â€کyan takardu ba, sai dai an kyautata bayani a cikinsa da kuma kyawun zabin bayanai da lura da abubuwan da suke masu tasiri na musamman a cikin zukata, hada da nau’in tsarin da aka yi masa. Kuma yana daga cikin abin da ya kamata a yi nuni da shi cewa irin yadda nan da nan daga sanya shi kasuwa sai ya kare da wuri ba tare da wani tallata shi da muka yi ba a cikin jaridu ko a wani taro, an kai shi kasuwa ne kawai kamar yadda aka saba, kamar yadda yake a bisa al’ada.

 Wannan al’amarin kuwa shi ne ya karfafa mu yin rubutu a cikin irin wannan maudu’i wanda yake mahallin cece-kuce tsakanin bangarorin mazhabobi da darikokin musulmi. Sannan kuma akwai fatan ganin an samu farin cikin muminai a cikin wannan lamari ga wanda da yake neman yardar Allah kuma yake neman ganin an kawar da kiyayya ta hanyar kawo abubuwan da aka yi tarayya a tsakanin musulmi a cikin dukkanin fagagen ci gaban musulunci wanda ya shafi hukucnin shari’a ko akidarmusukunci ko tarihin musulmi, kuma ta yiwu mu kara da cewa yana iya zamantowa cewa birorrukan marubuta masu tsafta suna iya kasancewa hanyar da zata kasance mai rabauta ga hidimar musulmi kuma mafi kyawun hanya domin samun fahimta tsakanin musulmi.

 Wannan kuwa hada da cewa wannan hanyar tana iya yanke hannayen hanyoyin nan na â€کyan barandan makiya da suke karbar kudade domin ganin sun kawo yamutsi da hura wuta da yada kiyayya tsakanin al’ummar musulmi kamar yadda muna iya ganin haka a wasu wurare lokaci bayan lokaci, wanda wannan al’amari ne da yake ba mu tabbacin cewa lallai akwai wasu hannayen marubuta masu bin â€کyan jiya da ba su gushe ba suna irin wannan mummunan aiki a duk lokacin da suka samu dama.

Kuma ina maimamaita abin da ya gabata a cikin bugu na daya cewa idan an samu wani kalami ko wata magana maras dadi a cikin bayanina to ba yana nufin domin gaba ne ko kiyayya ba, ina neman tsarin Allah daga irin wannan fushi da bai kasance domin imani ba ko kuma nuna fushi kan abin da ya shafi hadin kan musulmi ko kuma wani abu da zai nuna halaccin irin wannan usulubi.

To tunda kamala cikakkiya ta kasance ga Allah ne shi kadai, kuma mutum yana da tawaya, don haka ne ma kokarin ganin ya samu dadi a cikin wannan kamalar tasa ya kasance daga al’amuran da ake so, don haka ne ma sai na mike tsaye wajen ganin na gyara wannan rubutu da kuma yin wasu kare-kare da nake ganin zasu kamala wannan Littafi, kuma ina sanar da mai karanta wannan littafin da cewa yana da kyau ya kalli wannan littafin da kallon da yake na nakadi na ilimi, ba irin na iface-ifacen nan na masu son zage-zage ba wadanda suke jifan waninsu da wani abu da suke da shi wanda shi wanda suke jifa din ba shi da shi, sai dai son rai ne ya rufe idanuwansu ya kurumtar da su.

Abin da aka fada ga me da wani mutum kwarai ya kayatar da ake cewa da shi me ya sa kuke canza "K" da "G", kuma kuke canza "Dh" da "Z" (wato suna canza ط° da ط² su kuma canza ظ‚ da Ø·Ø›) sai ya ce: "ظ†ط­Ø¸â€  ظ„ط§ظ†ط؛ظˆظ„ ط²ظ„ظƒ"

 Daga karshe ina neman wanda ya karanta wannan littafin ya fadakar da ni idan ya ga wani aibi ko wata zamiyar kafafu, domin mumini madubin mumini ne. Allah ya shiryar da mu ga abin da yake so kuma yake yarda da shi, kuma muna godewa Allah tun farko har zuwa karshe.

 



1 2 3 4 5 6 next